19/06/2024
A Gobe Alhamis 20/6)2024, Kungiyar Mai Mala Buni Solidarity Movement Karkashin Jagoran Cin Shugaban Kungiyar Kollon Kafa ta Yobe Desert Stars, Hon Mohammed Alkali Accama Sarkiyo, Garkuwan Matasan Fika Kuma Sarki 10 Zamani 10 ta Shirya Raba jersey da Kollaye a Kungiyoyi Sama da 10 a Garin Geidam a Madadin Mai Girma Gomnan Jahar Yobe.
Kafin Rabiyar Za'a Buga Wasa na Musamman Domin Nuna Goyon Baya ga Gomnatin Mai Mala Buni CON, Bisa ci Gaban da ta Kawo Akan Matasan Jahar Yobe Tsakanin, GEIDAM ACADEMY FC 🆚 FC PORTO GEIDAM a Filin Wasa na Kafela Primary School Geidam da Misalin Karfe 4 na Yamma.
11/06/2024
Za'a Buga Wasan ne Gobe Laraba a Filin Wasa na Ajari United Damaturu.
08/06/2024
A gobe lahadi 9/6/2024, za'a fara buga gasar AAJ FOOTBALL TOURNAMENT, a shiyar Yobe ta arewa (ZONE C) wanda za'a kece reni tsakanin NGURU ACADEMY da BADE ACADEMY a fili wasa na NGURU TOWNSHIP STADIUM.
Babban bako na musamman shine captain na super eagles Ahmed Musa, bayan shi ana sa ran zuwan manyan baki daga sassa daban-daban na Nigeria.
Ina kake goyon baya kuma meye fatan ka ga wanda ya daura gasar ?
30/05/2024
Ana Kira ga Shuwagabannin Kungiyoyi, Masu Horarwa da Sauran Masu Ruwa da Tsaki na Kungiyoyin Kwallon Kafa na Jihar Yobe, Cewa an Kara Lokacin Register (Affiliation) da FA na 2023/2024 Daga 5/6/2024 Zuwa 12/6/2024.
Sanarwar na maganane akan sabun ta biyan kudin register da Yobe Football Association (F.A) na kakar 2023/2024.
Sanarwar ta fito ne daga sakatariyar Yobe Football Association, (Yobe FA) ta hannun shuwagabannin kungiyar s**a umurce ni da in rubuto tare da sanar da ku cewa, an tsawaita lokacin yin register (affiliation) da ake yi da kungiyar FA.
Anyi haka ne domin baiwa kungiyoyin da basu yi register (affiliation) ta shekarar 23/24 da FA, wanda kungiyar ta sanya ranar 5 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuni 2024 domin tabbatar da kungiyoyin da basu yi register ba sunyi.
Ali Alhaji Mellah Dre
F.A Media Officer
28/05/2024
SANARWA !! SANARWA !! SANARWA !!
Ana sanar da yan wasan Damaturu United FC cewa akwai training daga yau talata har zuwa ranar alhamis a filin wasa na Damaturu Academy.
Sannan ana kara sanar da yan wasan cewa a wannan makun ne kungiyar zata cire final list na yan wasan da zasu jagoranci Damaturu local government a gasar Governor's Cup 2024, sabi da haka kar dan wasa yayi fashin zuwa training.
SANARWA DAGA
HEAD COACH; MALAM AMADU GUGA
22/05/2024
Wasan sada zumunta tsakanin DAMATURU UNITED FC DA NAYI-NAWA SELECTION FC da za'ayi gobe alhamis, an canza zuwa filin Ajari United Damaturu.