15/07/2026
MUHAWARA!
Magoya bayan Real Madrid sun shiga hauma-hauma sun rasa tudun dafawa tun bayan kora kasashen Brazil, Portugal da Faransa daga kofin duniya. Yanzu haka Ingila ce kadai ta rage a gasar da akwai dan wasa guda na Real Madrid a ciki, sai Cucurella dake wakiltar Spain amma ko atisaye bai taba yi da kulob din ba, Jude Bellingham, kuma a ranar Larabar nan da misalin karfe 8:00 na dare za su fafata da Argentina.
TANGA SPORTS 360
15/07/2026
Duk da cewa Lamine Yamal ya yi bajinta wajen zura daya daga cikin kwallayen da za su iya zama mafiya kayatarwa a kofin duniya ta bana, amma alkalin wasa ya soke kuma bisa ga dukkanin alamu ba satar gida bace kuma VAR bana yi wani yunkuri na nuna wa duniya zahirin abundant faru ba.
A ganin ku an yi wa Lamine adalci wajen soke wannan kwallo?
TANGA SPORTS 360
15/07/2026
Ko jajjagen da Spain da yi wa France zai bata damar lashe kofin duniya a bana?
TANGA SPORTS 360
15/07/2026
Nawa da nawa za a tashi wasa tsakanin Ingila da Argentina?
TANGA SPORTS 360
14/07/2026
Nawa da nawa za a tashi a wasa na farko na zagayen gaf da karshe da za a barje gumi tsakanin Faransa da Andalus?
Wacce kake so ta kai wasan karshe……….Mbappe ko Lamine?
TANGA SPORTS 360
13/07/2026
Wanne ya fi kowa cikin wadannan ‘yan wasan tsakiyan?…………….shirya mana sunayen su daga na daya zuwa na 5 bisa kwarewa da gogewarsu a kwallon kafa. ‘Yan wasan sun hadar da; Declan Rice, Bruno Fernandes, Jude Bellingham, Pedri da Vitinha.
TANGA SPORTS 360
13/07/2026
Tare da la’akari da kasashen da wadannan ‘yan wasan su ka fito, wacce kungiyar kwallon kafa ce wannan?
A rubuta mana sunan kungiyar a comment section👇🏽
TANGA SPORTS 360
13/07/2026
Arsenal na son kammala cinikin dan kasar Argentina, Julian Alvarez, kafin ta tafi wasannin motsa jiki (pre-season). Kungiyar ta birnin Landan ta karkata akalarta kan dan wasan na Atletico Madrid ne bayan PSG ta shaida mata cewa, Bradley Barcola ba na sayarwa bane.
Barcelona ta matsa kan Alvarez amma Atletico Madrid ta yi kememe wajen bata damar tattauna batun komen tsohon dan wasan na Manchester City zuwa yankin Catalan.
TANGA SPORTS 360
12/07/2026
Kasar Uruguay ta tabbatar da nadin tsohon dan wasan kungiyoyin Manchester United, Atletico Madrid da Villarreal, Diego Forlan a matsayin sabon kocin babbatar tawagar kwallon kafa da ke wakiltarta a wasanni na kasa da kasa.
Forlan, wanda ya lashe takalmin zinare na yawan cin kwallon a kofin duniya ta 2010, zai jagoranci babbatar tawagar kasar ne da kuma ta ‘yan kasa da shekaru 20 a lokaci guda har zuwa Maris din 2027.
TANGA SPORTS 360
12/07/2026
Shirin faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Maza zuwa ƙasashe 64 zai samu cikakken nazari ne bayan kammala Gasar Kofin Duniya ta 2026, inda shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya bayyana cewa ya kamata gasar ta kasance “ta duniya baki ɗaya” kuma ta ba ƙasashe da dama damar shiga.
An fara gabatar da wannan shawara ne a bara, kuma Infantino ya ce nasarar da aka samu daga sabon tsarin gasar mai ƙasashe 48 ya nuna cewa lokaci ya yi da FIFA za ta duba yiwuwar gudanar da gasar zuwa ƙasashe 64.
A cewarsa, Kofin Duniya na farko da aka buga a tsakanin ƙasashe 48 ta kasance babbar nasara, inda ya yi nuni da cewa ƙasashe tara cikin goma daga nahiyar Afirka sun kai zagayen ’yan 32.
A shekarar 2017, FIFA ta amince da ƙara yawan ƙasashen da ke halartar gasar daga 32 zuwa 48.
A watan Afrilu na 2025, Hukumar Kwallon Kafa ta Kudancin Amurka (CONMEBOL) ta gabatar da ƙudiri a hukumance na faɗaɗa gasar ta 2030 zuwa ƙasashe 64, amma har yanzu FIFA ba ta yanke hukunci kan batun ba.
Za a gudanar da Gasar Kofin Duniya ta 2030 ne galibi a Spain, Portugal da Morocco, yayin da za a buga wasannin buɗe gasar guda uku na farko a kasashen Argentina, Uruguay da Paraguay, domin bikin cika shekaru 100 da fara Gasar Kofin Duniya. Kasar Uruguay ce ta karɓi bakuncin gasar ta farko a shekarar 1930.
TANGA SPORTS 360