13/07/2026
🚨🗣️ Luis de la Fuente: "Faransa ta fi ƙarfin da take da shi lokacin da muka haɗu da ita a baya. 'Yan wasansu sun ƙara bunƙasa sosai."
"Mbappé ya fi da, Dembélé ma ya fi da... kuma a matsayin ƙungiya gaba ɗaya sun fi ƙarfi yanzu. Amma mu ma mun samu ci gaba sosai." 🇪🇸🇫🇷
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🚨 SABON LABARI: Rahotanni sun ce AS Roma ta aika wa Chelsea tayin ɗaukar Alejandro Garnacho.
Tayin ya ƙunshi: £4.2m domin aro na kakar wasa guda tare da zaɓin saye na dindindin kan £30m.
Haka kuma, bisa ga rahoton Gianluca Di Marzio, wannan zaɓin sayen na iya zama tilas idan wasu sharuɗɗa da aka gindaya s**a cika.
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🚨🗣️ Xabi Alonso: "Na yi magana da Enzo Fernández. Ina son ya ci gaba da zama a Chelsea."
— 'ar Wasanni
13/07/2026
An tambayi Kounde: "Shin ka ji Lamine ya nuna maka rashin girmamawa?"
🗣 Jules Koundé: "A'a, ko kaɗan ban ji ya nuna mana rashin girmamawa ba. Na san Lamine sosai, kuma wannan dabi'arsa ce."
"A ganina, abin da ya yi kawai wani abu ne da ya fito kai tsaye ba tare da shiri ba. Haka yake yi a Barcelona ma, don haka babu wata ma'ana ta daban a cikin abin da ya aikata."
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🚨 DA ƊUMI-ƊUMI: Mason Greenwood ya ƙi amincewa da sabon tayin Al-Ahli na albashin Yuro miliyan 12 (€12M) a kowace shekara.
Yanzu komawar Greenwood zuwa Fenerbahçe ta kammala gaba ɗaya. Ya amince da dukkan sharuɗɗan kwantiraginsa bayan ya yi watsi da tayuka da dama daga ƙungiyoyin Saudi Pro League.
Bayan Al-Ahli ta kasa ɗaukar Greenwood, ta koma kan ɗan wasan Portugal Francisco Trincão a matsayin madadinsa, kuma ana sa ran zai taka leda a matsayin winger.
Majiyar Labari: [Sacha Tavolieri]
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🏆 A cewar Opta, Argentina ce ke da mafi ƙarancin yiwuwar lashe Kofin Duniya a cikin ƙasashe huɗun da s**a kai wasan kusa da na ƙarshe (Semi-final).
1. 🇫🇷 Faransa — 34%
2. 🇪🇸 Sifaniya (Spain) — 24%
3. 🏴 Ingila — 23%
4. 🇦🇷 Argentina — 20%
Me za ku ce? 🤔
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🚨🗣️ Ahmed Fatouh (Masar): "Da can ina matuƙar son Messi, amma bayan wasan da muka yi da Argentina, ban ƙara son sa ba, kuma bana fatan ya sake lashe komai har abada."
"An yi mana rashin adalci. Mun rasa hankali a mintuna 10 na ƙarshe, kuma an ƙwace wasan daga hannunmu." 🇪🇬💔🇦🇷
— 'ar Wasanni
13/07/2026
🚨❌ A cikin dukkan 'yan wasan gaban Barcelona, Lamine Yamal kaɗai ne ba a shirye kungiyar ta ke ta sayar da shi ba.
Koci Hansi Flick na son yin babban sauyi a sashin harin ƙungiyar, inda ake sa ran za a sake fasalin layin gaba gaba ɗaya.
Wannan na nufin duk sauran 'yan wasan harin Barça na iya barin ƙungiyar idan ta samu tayin da ya dace, amma Lamine Yamal shi ne kaɗai ake kallon ba za a taɓa sayar da shi ba.
Majiyar Labari: [MARCA]
— 'ar Wasanni