31/08/2026
🔵 | ALONSO IS A BLUE, haka s**a rubata mai..
Duk da rashin bugawa Chelsea wasa da baiyi ba, amma sunyi hotonsa bayan wasanni uku kacal!
A daidai wannan lokaci shekara guda da ta wuce, Alonso yana Real Madrid yana ƙoƙarin aiwatar da ra'ayoyinsa tare da ƙungiyar da ya girma domin tallafa mata.
Yanzu kuma Chelsea baki dayanta, mamallaka da magoya baya, sun dauki yarda da ragamar Chelsea baki daya sun dorawa mai.
Allah ya bashi nasara akan wannan aiki da ya dakkowa Chelsea.
30/08/2026
Raunin Caicedo da fitarsa daga filin wasa da hawaye a idanunsa na iya kawo mana cikas a gaba daya kakar wasa!
Duba da irin wannan raunin, dukda cewa ba’a fadi sakamakon raunin ba har yanzu, amma irin wannan yanayi yana da matukar wahala sosai.
Chelsea na rasa inganci da nagarta a tsakiyarta, duba da rashin Caicedo da kuma rashin Enzo.
Muna buƙatar karin siyan 'yan wasa biyu a tsakiya, komai tsadar da su, kafin rufe Transfer Market, ko da kuwa... Enzo zaici gaba da zama a Chelsea!
Akwai ɗan wasa Lamine Camara kawo shi Chelsea ya zama dole - tare da buƙatar wani ɗan wasan tsakiya.
Muna fatan Xabi da Mamallaka Chelsea zasu duba wannan lamari.
30/08/2026
🔵 Xabi Alonso a wasanmu na jiya yayi aikin kwakwalwa, aiki tukuru sosai.
Alonso ya canja salon wasanmu akan Brighton, inda yaki yarda mu fuskance su a yadda suke son yin wasa da mu.
Maimakon mune ya kamata muyiwa Brighton wasa tunda a gidanmu suke, kuma munfi su karfin ‘yan wasan, amma Alonso sai yace da su ku karbi kwallon, mu kuma zamuyi muku Attacking mai zafi, kamar dai yadda suke mana.
Kungiyar Brighton tana ɗaya daga cikin kungiyoyi mafi wahala, tayi fice wajan zuwa da abin mamaki a gasar Premier ta Ingila.
Zaku iya tunawa sau hudu a jere muna shan kashi a hannunsu, kuma abin mamakin a wasani ukun ƙarshe na gasar Primier a kowanne wasa kwallaye uku suke zura mana, a jiya lahadi ma sai da s**a zura mana kwallaye uku!
Godiya ga Allah da wannan Nasara da muke samu, All ka karo mana dubunta.
Let’s go Blue💙
29/08/2026
🚨📝 | Jaridar The Guardian:
"Akwai tsoro game da Sanchez ko zai yarda a matsar da shi gefe guda da zarar sabon gola yazo, amma Chelsea ba tayi la'akari da damuwar wasu ba."
"Lokaci yayi kadan, dole ne Sanchez ya tafi, saboda gefe za’a matsar da shi, idan yaci gaba da zama a Club din, kuma da wuya ya buga wasan Brighton."
"Akwai nuna bukatar Sanchez daga Ingila, Turai, da kuma Saudiyya."
"Wannan ita ce rayuwa, Chelsea ta yanke hukunci."
.
29/08/2026
🚨 A Videon da Fabrizio Romano ya saka jiya ya bayyana cewa..:
Akwai tsammanin cewa Enzo bazai buga wasan da Chelsea zata buga da Brighton na wannan makon ba, kamar yadda bai buga wasan kungiyar da Luton Town a makon da ya gabata ba.
Me yasa? Domin Enzo a halin yanzu yana da burin canja wuri zuwa Man City, kuma a halin da ake ya rigada yacewa Man City ya amince.
Saboda haka, duk lokacin da Xabi Alonso ya sanya ɗan wasa a filin wasa sanye da rigar Chelsea domin wakiltar kungiyar, toh yana son wannan ɗan wasan ya kasance mai himma 100%.
A yanzu akan Fernandes, lamarin har yanzu yayi tsamari, a inda ya zama dole a jira aga abin da zai faru tsakanin ƙungiyoyin biyu.
Ɗan wasan yana cikin ƙoshin lafiya, amma babu tsammanin zai buga wasan..
Let’s go Blue💙
28/08/2026
🎚 - Daga ƙarshe dai ansami yarjejeniya wacca tayi daidai da kusan bukatunsu, game da sponsoring gaban rigar. ✅😭
Chelsea ta sanya hannu kan yarjejeniya tare da kamfanin USDC , domin daukar nauyin tallata kamfanin a gaban rigarsu.
Wannan yarjejeniya ta iya kakar wasa ɗaya ce kacal, akan kudi fam miliyan 50, amma akwai damar kara zaɓin tsawaita kwantiragin.
USDC kamfani ne na cryptocurrency da hannun jari da ke kasar Amurka.
Wannan labari ne mai daɗi, domin mun gaji da ganin gaban rigar haka empty babu komai.
Amma kuna ganin wannan rubutun yayiwa gaban rigar kyau kuwa?
Let’s go Blue💙
27/08/2026
📆 | YAU ALHAMI, Chelsea zata karbi bakuncin kungiyar kwallo kafa ta Luton Tow, domin barje gumi na fafatawa a cikin gasar tseren cin kofin cikin gida na Ingila, Carabao Cup.🏆
HOME MATCH🏟
⚽️ | Fafatawa - CHELSEA 🆚 LUTON TOWN
🏟 | Filin wasa - Stamford Bridge.
⏰ | Lokaci - Karfe 7:30 daidai Agogon Nigeria🇳🇬 da Niger🇳🇪.
🚩 | Alkalin wasa - Elliot Bell
Duk wanda yaci wasa a wannan fafatawar, zai hadu da kungiyar Leed United.
Nasara ga Chelsea ako da yaushe.🤝👏
Let’s go Blue✊💙
Come on Chelsea🤝
26/08/2026
🚨 - LABARI DA DUMI-DUMINSA.. Emiliano Martínez zuwa Chelsea🥳
Wakilan dan wasan na Argentina sunyiwa Chelsea tayin Golar ga kungiyar, kuma zuwa yanzu Chelsea ta bude shafi na tattaunawa domin daukar mai tsaron ragar Aston Villa Emiliano Martínez.
Fabrizio romano ya bayyana cewa; Chelsea na la'akari da wannan zaɓin a matsayin abinda kan iya jewa ya dawo a makare, ko kuma bisa ga abin da zai faru da sauran gola ɗinsu.
Fabrizio ya kara da cewa Emiliano Martínez zai kasance cikin shiri, zai cewa Chelsea Eh, koda ba tare da buga gasar Zakarun Turai ko ƙwallon ƙafa ta Turai ba.
26/08/2026
🚨🗣️ Xabi Alonso Primier ko Laliga wacce gasa ce tafi sauƙI..
Mai rahoto: "Xabi, bayan nasarar farko a Premier League, wacca gasa ce tafi sauƙi a wajan samin nasara, nan ko La Liga?"
Xabi Alonso: "A La Liga, ƙananan ƙungiyoyi suna barin manyan ƙungiyoyi su sarrafa wasa, su zauna su kare gida, gasar Premier kuma ba ta da tabbas.
"A nan, zaka iya kasancewa cikin iko na mintuna biyar, amma abu na gaba da ka sani, zaka tsinci kanka kana fafutukar kare gidanka ne, Fulham sun nuna basa jin tsoron kai hari da ƙwallo, kuma hakan yayi musu amfani.
"Kowace ƙungiya a gasar Premier tana fafatawa akan yin nasara. Sun shirya yin gaba da gaba da manyan ƙungiyoyi, domin samun maki uku, a maimakon zama a baya, yin wasa da ƙarancin tsaron gida, da kuma kare burinsu.
"Naji daɗin wasan, kuma zuwa yanzu, idan haka ƙwallon ƙafa take a kowane mako, nafi son ta a nan."