07/08/2026
Bayan da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Deportivo Municipal da ke kasar Peru ta fuskanci koma baya da dama na fadawa rukuni na biyu tare da shiga matsalar kuɗi, hakan ya ta yanke shawarar saka talla guda 1,000 a jikin rigarta ta kakar 2026/27, inda kowanne tallah aka sayar da shi kan dala 60 kacal.
Wannan matakin ya taimaka musu wajen tara isassun kuɗaɗe da za su gudanar da wasannin su a gasar Copa Perú 🇵🇪🤯
Sakamakon haka, an samar da ɗaya daga cikin rigunan ƙwallon ƙafa mafi ban mamaki da tarihi a duniya 🔥
07/08/2026
🚨⚪ Rana ta farko ga Yan Diomande a sabuwar kungiyar sa ta Real Madrid! 😃🤙
07/08/2026
‼️💥 LABARI: Rodri Hernández zai rika samun Yuro miliyan 27.5 a kowace shekara a FC Barcelona, ciki har da ƙarin kuɗaɗen alawus-alawus, bayan an cimma yarjejeniya kan dukkan sharuɗɗan da s**a shafi ɗan wasan.
Kunshin albashin ɗan wasan tsakiyar na ƙasar Spain ya ƙunshi albashi na dindindin na Yuro miliyan 17.5 a shekara, tare da ƙarin alawus na iya kaiwa Yuro miliyan 10 bisa la’akari da nasarorin da ya samu shi kaɗai da kuma na ƙungiya, ciki har da ƙarin lada idan an lashe gasar Zakarun Turai (UEFA Champions League) ko kuma ya samu nasarar lashe Kyautar Ballon d’Or.
Rodri zai zama ɗan wasa na biyu mafi yawan albashi a Barcelona, bayan Lamine Yamal kaɗai, inda zai rika samun albashi fiye da Raphinha, Pedri da Frenkie de Jong.
A yanzu Barcelona na mayar da hankali wajen kammala yarjejeniya da Manchester City kan kuɗin sayen ɗan wasan, yayin da Rodri ke jiran izinin tafiya Barcelona domin kammala komawar sa.
07/08/2026
🚨 Bayern Munich karkashin jagorancin Vincent Kompany ta doke Aston Villa da ci 2-1 a wasan sada zumunta na share fagen fara kakar wasa ta bana, inda suke ci gaba da shirye-shirye domin tunkarar sabuwar kakar da ake saran farawa nan da bada jimawa ba
07/08/2026
Barcelona na fatan kammala cinikin Rodri nan ba da jimawa ba, inda ake sa ran Rodri zai isa kungiyar a ranar 12 ga watan Agusta.
07/08/2026
🚨🔵🔴Ferran Torres kan matakansa na gaba: “Abin da na sani shi ne zan dawo atisaye tare da Barcelona nan ba da jimawa ba. Sai mu ga abin da zai faru.” In ji shi yayin wata hira da ya yi da kafar labarai ta CNN. 🧨
07/08/2026
💪🏾😲 Sauyi mai ban mamaki a yanayin jikin Rodrygo. Dan wasan gefe na Brazil ya ƙara yawan girman jikin sa sosai a lokacin da yake murmurewa daga raunin da ya ji. 🇧🇷
Yana son komawa fagen wasa cikin mafi kyawun yanayi domin taimaka wa Real Madrid karkashin José Mourinho. 😤⏳
07/08/2026
🚨AN KAMMALA YARJEJENIYA : LA Galaxy ta cimma yarjejeniya domin ɗaukar tsohon ɗan wasan bayan Barcelona da Como, Sergi Roberto dan asalin kasar Spainia ✨🇺🇸🗞️
Sergi Roberto ya bar ƙungiyar Como a matsayin ɗan wasa na kyauta a wannan bazarar, kuma yanzu zai ci gaba da buga ƙwallonsa a gasar MLS bayan da kungiyar Galaxy ta kammala daukar sa a kyauta 💰
07/08/2026
Yan wasannin gaban ake sa ran Real Madrid za ta yi amfani da su a kakar 2026/27 inda ake ganin zasu zama masu matuƙar bada tsoro ga yan wasan bayan da zasu tunkara
Bayan kammala daukar dan wasa Yan Diomande, yanzu mai horaswa José Mourinho yana da zaɓuɓɓuka masu yawa da ban mamaki a ɓangaren kai hari na kungiyar
07/08/2026
An fitar da yadda wasannin mako na farko zasu kasance a gasar (NPFL) ta bana 🏆
inda ake saran fara gasar a ranar 28 a ga wannan wata na Agusta da muke ciki 🗞️
A ganin ku wanne wasa ne zaifi jan hankali ?