23/06/2026
Printy #10
FOOTBALL CLUB
23/06/2026
Printy #10
13/06/2026
SAN TURAKIN KANO, HAKIMIN KUNYA CUP
KUNYA UNITED F.C
v
F.C MATASA
Time :- 4:45pm
Date :- Saturday 13th June 2026
Venue :- Ambassadors field.
11/06/2026
17/4/2006 ( 20years ago )
TUNA BAYA MAI DAƊI ⚽🏆.
Ga tsohuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta KUNYA UNITED a lokacin da take kan ganiyarta tana girgiza filayen wasa da bajintarta. Wannan hoto ya ɗauko wani lokaci na musamman yayin da 'yan wasan ke shirin buga wasan hammaya da kungiyar All Star kunya a lokacin akwai haɗin kai da jajircewa.
Lokaci ne da magoya baya ba za su taɓa mantawa da shi ba. Kunya united ta rubuta tarihi, ta bar tarihin da har yau ake alfahari da shi.
Waye daga cikin 'yan wasan da kuke iya ganewa a wannan hoto?
A wannan wasa an tashi kunen doki
Kunya united 2 vs All Star 2
Abba croach da Ali Wada canavaro kowa ya jefa kwallo biyu a raga.
Wadansa s**a rasu daga cikin wannan hoto sun haɗar da
Sa'idu Kura
Aminu Yar Mamu
Alanso Goburawa
Aladuwa
muna addu'ar Allah ya jikansu ya kyautata makwancinsu, Allah yayi musu rahama da gafara ameen.
Mai rahoto: Engr saifullahi zangi Almustapha tsohon Dan ball a kunya united.
06/06/2026
Get well soon In sha Allah Lawan Kunya
06/06/2026
Press released.
Sanarwa ga manema labarai zuwa ga al'umma.
Kunya United kungiya ce mai tsari da hadin kai, da ta shahara wurin samar da tsaruka musamman wurin shirya wasanni ko yan wasa.
A kwanakin baya mun samu takardar neman izinin shiga kungiyar Kunya United daga dan wasa Abdulhamid Ibrahim Guida, inda ya nemi izinin mahukunta domin su bashi damar kasancewa da wannan kungiya kamar yadda zaku gani a takardar da zamu rarraba ga manema labarai.
Muna masu sanar da manema labarai da al'umma cewa Kunya United na tafiya ne akan tsari wanda muke fatan zai samar da gagarumin sauyi a duniyar kwallon kafa irin tamu tanan, musamman kan batutuwan da s**a fi kawo rudani irin na musayar yan'wasa.
A karshe muna yiwa Abdulhamid Ibrahim Guida fatan alkhairi bisa yadda ya nuna sha'awarsa ga kungiyarmu, hakan ya sake tabbatar mana da tsarin da muke tafiya akai yana kyau kwarai da gaske, muna yi masa fatan alkhairi da fatan kammala wasanni lafiya.
Sanarwa
Ibrahim Hashim Saad
DG Media & Publicity Kunya United.
A madadin,
Kunya United Management.
Asabar, 6th, jan, 2026.
��
06/06/2026
a wasan SAN TURAKIN KANO HAKIMIN KUNYA CUP mun tashi kunnen doki tsakanin Kunya United 0 da F.c Sila 0 a wasan rukunin B zagaye na biyu.
A halin yanzu Eagle ce ke jan ragamar rukunin B da maki 6, Kunya United na matsayi na biyu da maki 4, Sila tana mataki na uku da maki 1 sai Kunya Ocean da Matasa a mataki na hudu da na biyar da maki 0.
SAN TURAKIN KANO HAKIMIN KUNYA CUP
Kunya United
v
F.C Sila
friday 5th june 2026.
03/06/2026
TODAY FIXTURES
Kunya United v F.c 7 Stars ( ☆☆☆☆☆☆☆ )
Venue :- Kunya Filin tasha
Time :- 4:30pm
Date :- 3rd june 2026.
27/05/2026
Final result.
Kunya United 1
v
Kunya Ocean 0