Asadulhifz

Asadulhifz

Share

Passionate about knowledge & growth
� Lover of kind words and positivity
� Respect, honesty & good vibes only
� Living to inspire, not to impress

28/06/2026

Akwai darasi a wannan hoton kabarin na wani mutum mai suna Mai Ali Dogo.

An haife shi: 1908
Ya rasu: 1935

Ya rayu a duniya na tsawon shekara 27 kacal, yana matashi ya rasu.

Yau muna shekarar 2026.

Idan muka lissafa: Daga 1908 zuwa 2026 = shekara 118 kenan da haihuwarsa.

Daga 1935 zuwa 2026 = shekara 91 kenan yana cikin kabari. InnalilLahi Wa Inna Ilaihirrajuun.

Rayuwarsa a duniya shekara 27 ne kawai, rayuwar kabari kuma shekara 91

Dan'uwa Ka yi tunani...

Mutumin da wata rana yake tafiya, yana magana, yana dariya, yana cin abinci, yana da buri da mafarkai... yau shekaru 91 kenan yana kwance cikin kabari.

Ina gidansa? Ina motarsa? Ina dukiyarsa? Duka babu, abinda ya rage masa shine ayyukansa.

Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa:

"Ko wane rai zai ɗanɗana mutuwa." (Suratul Ali 'Imran: 185)

Ba wanda yasan ranar da zai mutu.

Wata rana kai ma za'a ɗauke ka daga gidanka, a yi maka wanka, a yi maka jana'iza, a kai ka kabari, sannan mutane su koma gidajensu, kai kuma a barka kai kaɗai a kabarinka tare da ayyukanka.

Ko da mutum bai mutu ba a yanzu har sai da yakai ranar tashin alƙiyama, to zai kasance a kabari har zuwa ranar da Allah Ya ƙaddara a busa ƙaho.

Ka tambayi kanka, me ka tanadar domin zaman kabarinka?

Allah Ka kyautata ƙarshenmu, Ka yalwata kaburburanmu da haske, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka sa mu kasance cikin bayinka na ƙwarai.

Amin Ya Rabbal 'Alamin.

© Salisu Abdurrazak Saheel

19/06/2026

Wani mutum yayi mafarki, acikin mafarkin sai yaga yayi Gona, ya shuka Masara gonar tayi kyau sosai, sai yaga Limamin masallacin Ka'abah Sheikh Abdur-Rahman Sudais yazo yana ta girbe amfanin gonar, sai yace haba Ya Sheikh, Masarar nan bata kai a girbe ta ba, yaya haka, Sheikh Sudais bai ce masa komai ba, ya cigaba da girbewa.
Bayan mutumin ya farka sai yaje wajen wani babban Malamin dake iya fassara mafarki ya tambaye shi fassarar wannan abinda ya gani acikin baccin sa.

Sai Malamin yace:
"Aiyukan ka na Lada ne ake ta girbewa ana bayarwa ma Sheikh Sudais din, domin mafarkin ka yana nuna kana da dabi'ar hassada ko Gulma".
Shin ka taba fadin wata mummunar magana akan Sheikh din ne?
Sai mutumin yace gaskiya shi bai taba yin wata mummunar magana akan Sheikh Sudais ba.
Shike nan sai ya tafi, yana ta tunani a zuciyar sa.

Bayan ya koma gida sai ya tuno cewa wata shekara da dadewa suna hira tare da abokan sa, ana hirar Malamai, sai yace ai karatun Sheikh Sudais ba dan Allah yake yi ba, yana yi ne don ace ya iya don duniya taji shi.
Amma idan kaji Sheikh Shuraim yana karatu zaka ji yana ratsaka zuciyar ka, zaka ji tabbas shi kam Sheikh Shuraim yafi yi domin Allah.

Sai ya koma ya fadawa Malamin ga abinda ya tuna ya taba fadi akan Sudais, sai Malamin yace to laifin kenan, mafi yawan aiyukan ka na Lada kayi hasarar su saboda wannan furucin da kayi akan sa.
Sai mutumin yace wallahi daga yau na tuba, kuma zan gyara, zan daina kage ko sharri akan mutane.
Malamin yace da ace ka mutu akan irin wannan 'dabi'ar da sai anje lahira kaga baka da Ladan komai b***e a kaika Aljannah.
Asadulhifz Shaikh Abubakar Gummi School Prof. Adam Muhammad Abubakar Adamu Musa Kore Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo Viral

18/06/2026

Duk shekara Musulmi yakan yi sujuda guda dubu 11,424 a cikin sallolin farilla kadai. Yi kokari ka inganta sallar ka. Sujuda daya tak aka ce Iblis yayi amma ya bijire, idan ka dace sujudar ka ta karbu ka sha kwana a wajen Ubangiji.

12/06/2026
12/06/2026

"Sadakar sirri (Sadakar da aka yi ta a boye) tana kawar da fushin Ubangiji".
🎤
Inji Manzon Allah (S.A.W).

Akwai mutanen da sun karye a harkar kasuwancin su saboda wani bangare na fushin Ubangiji ya shafe su, akwai wadanda suke cikin damuwa iri iri a yau saboda fushin Ubangiji ya taba su, akwai wadanda sun gagara samun nasara akan abinda suke nema a rayuwa saboda fushin Ubangiji, abinda zaka yi...👇

Ka nemi wani mutum ko wasu mutane kayi musu Sadaka a boye, kada ka bari wani yasan kayi musu, sai ka koma kayi addu'a ka roki. Wannan Sadakar ba lallai ta zama mai yawa ba, gwargwadon halin ka.
A yau zaka iya yin Sadaka wa mutum ba tare da ya sani ba, misali:

Zaka iya tura recharge card ta Bank application dinka, wanda ka tura masa ba lallai yasan kaine ba, wannan Sadaka ce ta sirri, zaka iya sayan Data wa mutum ba tare da ya sani ba. Zaka iya zuwa shagon POS ka bayar da account din mutum a tura masa, ba zai ga sunan ka ba b***e ya gane kai ne, wannan sadakar sirri ne.

Wanda kake binsa bashi zaka iya cewa wane na rage maka Naira dubu 3,000 daga cikin dubu 10,000 da nake binka, yanzu dubu 7,000 zaka bani idan kazo biya, wannan Sadaka ce ta sirri daga kai sai shi, ko kuma wane na yafe maka gaba daya ka barshi kawai, hanyoyin sadakar sirri suna da yawan gaske.

Zaka iya neman aika sako kace a bashi amma kada a fadi daga gare ka ne. Musamman a ranaku irin wannan ta Juma'a, Litinin da Alhamis, ka dinga yin haka zaka samu mafita akan al'amuran da s**a yi maka kunci, in sha Allah.

Photos from Asadulhifz's post 10/06/2026

Jiya Talata Alhaji Abdulmumin Yakubu Mai Shanu (AYM), mai kamfanin AYM Shafa Oil ya fitar da zakkar dukiyar sa ta wannan shekara, kuma ya rabawa mutane dari 500, kowannen su ya samu Naira dubu 200,000.

Naira miliyan 100,000,000 kenan.
AYM Shafa ya saba duk shekara yakan tsara fitar zakkar sa a nan Bauchi duk shekara bayan aikin Hajji.
Anyi rabon a nan cikin garin Bauchi.

Zakka tana daya daga cikin Ibadun da ake so ayi su a fili a bayyane.
Allah ya cigaba da tsarkake masa dukiyar tare da dukkan sauran masu wadata dake kokarin yin abinda Allah yace a duk inda suke.

09/06/2026

Ya Biyoni Inbox Yace Min....

Profesa Watarana Na Fito Sallar Azahar Ɓarawo Ya Sace Min Wayata Ƙirar Iphone 15. Bayan Na Dawo Office Na Shiga Damuwa Saboda Kuɗin Da Suke Cikin Account Ɗina.

Nan Take Na Kira Banki Aka Rufe Min Account Ɗina Baki Ɗaya. Sannan Na Tafi Bompai Na Biya Kuɗi Aka Fara Aikin Tracking Domin Nasan Yadda Aka Sace Min Wayata A Masallaci. 24hours Labari Yazo Min An Kamo Ɓarawon Wayata. Naje Na Ganshi Saurayi Mai Ƙarfi Ajika.

Na Tambayeshi Yadda Ya Sace Min Wayata Yace Yafi Kwana Sha Huɗu Yana Bibiyar Wayar Allah Bai Bashi Nasara Ba Sai Yau, Na Tambayeshi Sana'arsa Yace Min Sata, Nace Masa Meyasa Yake Sata? Yace Min Mahaifinsa Ya Rasu Ya Barsu Su Bakwai Shine Babba, Duk Duniya Ya Rasa Mai Taimaka Masa Ya Cigaba Da Karatu Saboda Haka Ya Ajiye Karatun Ya Nufi Sata Domin Kula Da Ƙannensa Mata.

Nan Take Nayi Umarnin Aje Gidansu A Bincika, Washe Gari Akaje Akazo Da Labarin Maganarsa Gaskiya Ce. Na Bashi 500k Nace Yaje Ya Siyawa Mahaifiyarsa Kayan Abinci, Sannan Na Umarci Kullum Ya Fito Yazo Kasuuwa Ya Zauna Idan An Tashi A Bashi 3k .

Tun Daga Wannan Ranar Bai Ƙara Sha'awar Ya Saci Kayan Wani Ba, . Nayi Imani Da Allah Cewa Yanzu Na Yarda Dashi Fiye Da Wasu Yaran Nan Nawa, Shiyasa Nake Kokarin Buɗe Wani Sabon Shago, Kuma Shi Zan Ajiye A Matsayin Manaja Insha Allahu Rabbi!

® Profesa Babuji
Asadulhifz Prof. Adam Muhammad Abubakar Shaikh Abubakar Gummi School Adamu Musa Kore Viral

09/06/2026

Hanyoyi 10 na Rage Damuwa

1. Yawaita ambaton Allah (zikiri)
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce: “Lalle da ambaton Allah ne zukata ke samun nutsuwa.” Ka yawaita tasbihi, istigfari da salati ga Annabi ﷺ.
2. Sallah da addu’a
Idan damuwa ta yi yawa, ka nemi taimakon Allah ta hanyar sallah da addu’a cikin tawali’u.
3. Karatun Alƙur’ani
Karatun Alƙur’ani da saurararsa na kawo natsuwa da kwanciyar hankali ga zuciya.
4. Karɓar ƙaddarar Allah
Ka yi imani cewa duk abin da ya same ka yana cikin hikimar Allah, kuma bayan kowace wahala akwai sauƙi.
5. Guje wa yawan tunanin abin da ya wuce
Abin da ya faru ya riga ya faru. Ka ɗauki darasi daga gare shi, sannan ka ci gaba da rayuwa.
6. Tattaunawa da mutanen kirki
da amintaccen mutum mai hikima na taimakawa rage nauyin zuciya.
7. Motsa jiki da tafiya
Tafiya, motsa jiki ko wasu ayyuka na taimakawa jiki da kwakwalwa su sami natsuwa.
8. Tsara rayuwa da ayyuka
Yawan rikice-rikice da rashin tsari kan ƙara damuwa. Ka tsara ayyukanka bisa fifiko da cancanata
9. kyautatawa da taimakon mutane
Sadaƙa da taimakon mabukata suna sanya farin ciki a zuciya kuma suna rage damuwa.
10. kyakkyawan fata
Ka yi imani cewa Allah zai buɗe maka ƙofofin alheri. Kada ka yanke ƙauna daga rahamar Allah.

Hikima

“Kada ka bari damuwar gobe ta hana ka jin daɗin yau, domin Allah wanda ya kula da kai jiya, shi ne zai kula da kai gobe.”

Allah ya yaye mana baƙin ciki da damuwa.

05/06/2026

An kawata duniya da abubuwa biyar:

1. Ilimi da malamai
2. Adalcin shugabanni
3. Ibadar bayin Allah
4. Amanar ’yan kasuwa
5. Kyakkyawar nasiha daga masu ba da shawara

Sai kuma Iblis ya zo da tutoci guda biyar domin ya lalata waɗannan abubuwa:

* Ya zo da hassada domin ya yaƙi ilimi.
* Ya zo da zalunci domin ya yaƙi adalci.
* Ya zo da riya domin ya lalata ibada.
* Ya zo da ha’inci domin ya lalata amana.
* Ya zo da yaudara da ruɗi domin ya lalata nasiha.

Darasi:
Idan aka kiyaye ilimi daga hassada, adalci daga zalunci, ibada daga riya, amana daga ha’inci, da nasiha daga yaudara, al’umma za ta kasance cikin alheri da zaman lafiya.

تفسير الرازي مفاتح الغيب 2/402.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Kano