Labaran wasanni

Labaran wasanni

Share

domin zafafan labaran wasanni kui mana follow da like

25/08/2026

Daukacin Team na Wannan gida, me suna [Labaran Wasanni] muna taya daukacin musulmin duniya murnar zagayowar Ranar haihuwar Manzon allah (S.A.W), muna masu yiwa annabi salati da fatan allah ya kara mana kaunar annabi da bin sunnah tasa, allah ya kara bamu zaman lafiya a dukkanin fadin duniya 🙏🏻

24/08/2026

🚨 PAUL POGBA YA RAGE FARASHIN GIDANSA NA ALFARMA DA ZE SIYAR

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Paul Pogba, ya rage farashin katafaren gidansa na alfarma da ke Cheshire [keshaya] yanki dake tsakanin Manchester da Liverpool daga £3.95m zuwa £3.5m a naira kudin kimanin naira bilyan shida ( 6 billion naira), bayan ya sha fama wajen samun mai siya. 🏡💰

Gidan mai ɗakuna biyar ya ƙunshi filin wasan ƙwallon ƙafa na cikin gida, gidan kallon fina-finai mai zaman kansa, dakin motsa jiki da kuma ɗakin kula da lafiya. 😮‍💨⚽

🗞️ labari daga MailSport

Photos from Labaran wasanni's post 20/08/2026

📰 ROBERTO CARLOS YA FADI GASKIYA KAN JITA-JITAR CEWA YA MUSULUNTA YA KARYATA ZANCEN, 'Yan JARIDA DA YAWA SUN YADA KARYA
Tsohon fitaccen ɗan wasan Brazil kuma gwarzon Roberto Carlos ya yi magana a karon farko kan jita-jitar da ta bazu cewa ya musulunta bayan aurensa da wata ’yar kasar Morocco mai suna Souhaila Al-Tahiri.
Rahotannin da s**a fito daga kafafen yada labarai na Turkiyya sun ce Roberto Carlos, mai shekaru 53, ya musulunta kimanin makonni huɗu da s**a gabata, bayan ya karanta Kalmar Shahada a wani taro da Sheikh Jihad Hamada, daya daga cikin fitattun ’yan kungiyar Musulmi a Brazil.
Abin da ya kara rura wutar jita-jitar shi ne wani rubutu da Ali Sahin, ɗan majalisar dokokin Turkiyya daga jam'iyyar Justice and Development Party, ya wallafa a shafin X.
Sahin ya bayyana cewa ya gana da Sheikh Jihad Hamada a São Paulo, inda Sheikh ɗin ya ce Roberto Carlos ya dade yana tuntubarsa, kafin daga bisani ya ziyarce shi makonni huɗu da s**a gabata, ya karanta Shahada sannan ya karɓi Musulunci.
❌ ROBERTO CARLOS YA KARYATA BATUN MUSULUNTARSA
Amma Roberto Carlos ya fito fili ya musanta wannan rahoto, inda ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa ya musulunta.
A wata hira da jaridar Saudiya ta Okaz ranar Laraba, ya ce:
“Ina matukar girmama Musulunci, kuma abin farin ciki ne ganin matata tana yin sallah, amma jita-jitar da ake yadawa cewa na musulunta ba gaskiya ba ce.”
💍 GAME DA AURANSA DA ’YAR MOROCCO
Roberto Carlos ya kuma bayyana cewa bikin aurensu ne ya sa mutane s**a fara zargin cewa ya musulunta.
Ya ce an gudanar da bikin aurensu ta hanyoyi fiye da ɗaya, domin an yi la’akari da addinai da imanin ’yan uwa.
Ya bayyana cewa wasu daga cikin ’yan uwansa Katolika ne, don haka aka gudanar da wani biki da ya dace da imaninsu, sannan aka kuma gudanar da wani biki da ya dace da matarsa da abokanta Musulmai.
A takaice: Roberto Carlos ya tabbatar da cewa yana matukar girmama Musulunci, yana girmama matarsa da addininta, amma ya ce labarin cewa ya musulunta ba gaskiya ba ne.

Photos from Labaran wasanni's post 15/08/2026

🔥 : Ronaldo Ya Dawo training Al Nassr Da Sabon Salon Gyaran Gashi! 🇵🇹🟡🔵

Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da Al Nassr a Riyadh, bayan hutun da aka ba shi bayan kammala gasar World Cup da kuma aurensa da Georgina Rodríguez.

✨ Ronaldo ya bayyana da sabon gashi mai launin Gold/copper, abin da ya bambanta da salon gyaran gashin da ya saba yi.

💍 Ronaldo da Georgina sun yi aure a Portugal ranar 11 ga watan Agusta, taron ya samu halartar ‘ya’yansu biyar.

⚽ Yanzu Ronaldo yana shirin sabon Season na wasanni a Saudi Pro League, amma rahotanni sun ce kocin Al Nassr, Ange Postecoglou, na iya ba shi lokaci kafin ya dawo wasa, domin kauce wa yiwuwar rauni bayan ya fara atisaye ne kawai bada jimawa ba sabida ya samu fitness sosai duk da ronaldo din dan wasane da be wasa da training koda lokacin hutunsa.

📅 Ana sa ran zai iya samun damar buga wasa a ranar 18 ga Agusta da Al Diriyah.

Ronaldo ya dawo! 🐐🔥

14/08/2026

🇭🇷 Ivan Rakitić ya bayyana irin MATSANANCIN MATSIN LAMBA da ake fuskanta a Barcelona daga yan jarida🤯🔵🔴

🗣️ Ivan Rakitić:

“Daya daga cikin wasannin farko na gasar La Liga bayan da na koma kungiyar Barcelona, mun doke Granada da ci shida ba ko daya 6-0. Na zura kwallo daya, sannan na taimaka aka ci ta biyu da kai.

Bayan an tashi wasan, yazama dole naje domin yin magana da manema labarai. Amma tambayar farko da aka yi min bayan mun ci 6-0 ita ce:

‘Me ya faru da ku yan wasan? Wataƙila farkon Sizin ne, amma har yanzu ba ku taka leda yadda ya kamata ba baku buga wasa mekyau...’ 😳

Sai na cewa yan jaridan wajen Mun ci 6-0, na zura kwallona ta farko a Nou Camp, mun yi nasara… amma tambayar farko ita ce, “Har yanzu ba ku taka leda yadda ya kamata 😂 🤯

Domin a Barcelona, ba wai kawai batun samun nasara ba ne...

🔥 akwai Batun ya kayi ka yi nasara cikin salon da ya dace. sannan dole ka buga wasa me kyau me burgewa🔵🔴

25/07/2026

Abun mamaki wani uba tare da yardar yan uwan sun radama yaron su suna Messi domin soyayyar su ga Lionel Messi na kasar Argentina 😱

22/07/2026

Sergio Ramos ya kwaikwayi salon daukar hoton messi akan gado kwance tare da world cup amma shi Ramos da world cup biyu ya dauka

22/07/2026

🚨 "Garnacho Yana da JiJi da Kai Irin ta Cristiano Ronaldo da Messi, Amma Bai da Kwarewa irin tasu" – Agbonlahor Ya Caccaki Shirin Aston Villa na son sayen Garnacho

Tsohon ɗan wasan Aston Villa, Gabby Agbonlahor, ya yi kakkausar s**a kan rahotannin da ke cewa Aston Villa na son ɗaukar Alejandro Garnacho.

Agbonlahor ya bayyana Garnacho a matsayin "wanda Manchester United da Chelsea s**a yi watsi da shi basa bukatarsa," sannan ya nuna shakku kan halayensa da rashin tabbas na kwarewar dan wasan. Ya kuma yi gargaɗin cewa ko da aro ne tare da sharadin saye daga baya, wannan cinikin zai iya zama babbar matsala ga Aston Villa, yana mai cewa Garnacho na iya kawo cikas ga haɗin kan 'yan wasan ƙungiyar ta Aston Villa.

Mafi ɗaukar hankali a kalamansa shi ne lokacin da ya ce:

«"daga abin da na gani a lokacin da yake Manchester United, Garnacho yana da girman kai irin na Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, amma bai ma kai ko kwarewar David Bellion ba Dan wasan Manchester United, wanda ya bugawa wa Manchester United Wasa kusan shekaru Ashirin 20 da s**a wuce."»

Duk da wannan s**a mai zafi, rahotanni na nuna cewa Aston Villa na ci gaba da ƙoƙarin ɗaukar Garnacho, inda kocin na Aston Villa Unai Emery ke da yaƙinin cewa zai iya farfaɗo da Kwarewar dan wasan.

Photos from Labaran wasanni's post 21/07/2026

🌟🔙 Capdevila ya sake dawo da al'adar sa'a da yayi lokacin World cup 2010! 🇪🇸🏆
Capdevila, wanda ya lashe Kofin Duniya tare da Spain a shekarar 2010, ya binne Kwandala a cikin ciyawar fili kafin fara wasan final din World cup 2010 suda kasar Netherlands shekaru sha shida16 da s**a gabata.
Jiya kuma ya zaɓi Marc Cucurella ya ya bashi kwandala ya binne domin ya maimaita wannan al'ada kafin wasansu da Argentina, saboda dukansu masu buga left-back ne wato gefen lamba uku. Cucurella ya binne wannan kwandala kafin a fara wasan, kuma daga ƙarshe Spain dince dai ta yi nasara. 🇪🇸🏆

Photos from Labaran wasanni's post 21/07/2026

🚨 Vini Jr ya yi tiyatar gyaran ƙasan haɓarsa (chin harmonization) a ƙasar Brazil, kamar yadda TMC Esporte ta ruwaito. 🇧🇷 � gyaran chin gyara ne na haba ko ince gabar da gemu ke fitowa in yayi kasa sai ai surgery ko ai cosmetics injection don dagoshi sai wanda kakeso

📸 Ga hotunan farko da aka ɗauka bayan an yi masa tiyatar.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kaduna?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Kano
Kaduna