30/08/2026
A ganin ku tausaya wa ce ga Irin halin da talakawan Najeriya keciki ne ko wata manufa daban?
📰 SASHEN LABARAN HAUSALINK MEDIA
Barka da zuwa Sashen Labaran HausaLink Media, inda muke kawo muku sahihan labarai cikin gaggawa da adalci.
Muna wallafa labaran siyasa, tattalin arziki, ilimi, lafiya
30/08/2026
A ganin ku tausaya wa ce ga Irin halin da talakawan Najeriya keciki ne ko wata manufa daban?
30/08/2026
Takarar shugaban cin ƙasar Nigeria.
23/08/2026
Iran ta ce zata kai kari kan kamfanonin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya muddin ta sanya mata takunkumi
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya fitar da wata sanarwar gargaɗi da ke bayyana cewa duk ƙasar da ta shiga cikin shirin takunkumin tattalin arzikin da Amurka ke shirin ƙaƙaba wa ƙasarsa, za ta fuskanci mataki mai tsanani.
Wannan jawabi na Rezaei ya zo ne biyo bayan sauyin shugabanci a Majalisar Tsaron, inda aka naɗa shi sabon sakatare da nufin tunkarar sabbin ƙalubalen da ke gaban ƙasar.
Wannan taƙaddama ta samo asali ne bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙaddamar wani sabon yaƙi ta fannin takunkumin tattalin arziki mafi tsanani a tarihi kan Iran.
Amurka na ƙoƙarin tursasawa abokan hulɗarta da sauran ƙasashn da ke alaƙar kasuwancin man fetur da Iran, musamman kasar China wadda ke sayen kashi mafi tsoka na man ƙasar, da su dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da ita.
A cikin jawabinsa, Rezaei ya jaddada cewa idan ƙasashe maƙwabta s**a goyi bayan Amurka, Iran za ta toshe Mashigar Hormuz da yankin Tekun Fasha baki ɗaya, ta yadda ba za a bar ko ɗigon ɗanyen ya fita zuwa ƙasashen duniya ba.
Ya bayyana cewa Iran za ta ɗauki duk ƙasar da ta taimaki Amurka a matsayin abokiyar gaba da za a shigar da ita cikin jerin ƙasashen da za a kai wa hari.
Haka itama gwamnatin Iran ta tsara matakai guda uku na mayar da martani, inda za ta fara da lallashi da tattaunawa da ƙasashen domin su janye jikinsu daga shirin Amurka. Idan har kasashen s**a ki amincewa da hakan, Iran ta yi barazanar ƙaddamar da hare-haren soji kai tsaye kan muhimman ayyukan tattalin arzikinsu domin durkusar da su.
22/08/2026
EFCC da ICPC sun gayyaci jami'an NFF kan badaƙalar Naira biliyan 12
Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC da ICPC, sun gayyaci wasu jami’an Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, dangane da bincike kan yadda aka yi amfani da Naira biliyan 12 da Gwamnatin Tarayya ta bai wa hukumar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a amince da ware kuɗin a shekarar 2024 domin biyan alawus – alawus da wasu hakkokin ƴan wasan tawagogin ƙwallon ƙafar Najeriya.
Ana sa ran jami’an NFF za su gabatar da bayanai kan yadda aka kashe kudaden da kuma wadanda s**a amfana da su.
Binciken ya kara jefa harkar kwallon ƙafar Najeriya cikin matsin lamba, a daidai lokacin da ake ci gaba da s**a da kiranye-kiranye da shugabannin na NFF su yi murabus sabon rashin taɓuka abin azo agani a wasannin baya-bayan nan.
Wannan na zuwa ne, yayin da ake ci gaba da matsa wa shugabancin hukumar ƙarkashin jagorancin Ibrahim Gusau ya yi murabus, bayan gazawar Super Eagles wajen samun tikitin gasar Kofin Duniya ta 2026 da kuma rashin nasarar Super Falcons a gasar neman gurbin Kofin Duniya ɓangaren mata na 2027.
Kwamitin wasanni na Majalisar Dattawa ya bayyana damuwa kan yadda ƙungiyoyin s**a yi fama da matsaloli a gasannin baya-bayan nan.
Wasu rahotanni sun kuma ce an bai wa shugabancin NFF wa’adin sa'o'i 24 da ya sauka.
17/08/2026
NDLEA ta k**a ƙwayoyi da darajarsu ta haura biliyan 3 a Najeriya
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta sanar da k**a wani ɗan kasuwar India ɗauke da muggan ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilogram dubu 1,550 a jihar Lagos
Hukumar ta kuma yi nasarar ƙwato ƙwayoyin da darajarsu ta kai naira biliyan 3 da miliyan 600 a jihar ta Legas, baya ga tarin wasu a jihohin Kano da Kwara da Edo da Filato da Oyo da kuma Delta.
Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun NDLEA Femi Babafemi ya sanyawa hannu kuma ya fitar a yau Lahadi.
Sanarwar ta ce baya ga ƙwace tarin muggan nau’ikan ƙwayoyin, hukumar ta kuma kame tarin masu safarar ƙwayoyin a sassan Najeriya, yayin mabanbantan ayyukan da s**a gudanar na baya-bayan nan.
Guda cikin mutanen da NDLEA ta k**a sun haɗa da Nwankwo Innocent mai shekaru 48 ɗauke da ƙwayoyi a Legas, sai kuma wani jagoran gungun masu safarar ƙwayoyi da hukumar ta kai samame gidansa, inda ta ƙwace ƙwayoyin da darajarsu ta kai naira miliyan 972,000,000.
17/08/2026
Jamal Musiala ya fuskanci wani abin firgitarwa a wasan Bayern Munich da RB Leipzig a Telekom Cup ranar Asabar, 15 ga Agusta 2026.
Musiala ya shigo wasan a rabin na biyu.
Ya ci kwallo a minti na 81, Bayern ta ci 3–1.
Bayan 'yan mintuna, ya fara nuna alamun jiri/rauni sannan ya fadi a filin wasa, abokan wasansa da likitoci s**a taimaka masa.
An danganta lamarin da zafin yanayi mai kusan 33°C da matsalar zagayawar jini, amma cikakkiyar diagnosis ba a bayyana ba.
Abu mai kyau shi ne ya tashi ya fita da kafafunsa, kuma daraktan wasanni na Bayern, Max Eberl, ya ce Musiala yana lafiya. �
Bulinews +1
A yanzu babu rahoton cewa ya sake samun wani babban rauni na kafa/ƙafa. Amma Bayern ba ta fitar da cikakken rahoton likita ba tukuna, don haka ba za a iya tabbatar da lokacin da zai dawo wasa ba.
12/08/2026
Babu wata barazana da gwamnatin tarayya za ta mini kan zaɓen ranar Asabar - Adeleke
Gwamnan jihar Osun kuma dan takarar jam'iyyar Accord Party, Ademola Adeleke, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ba ya tsoron ƙarfin gwamnatin tarayya ko goyon bayan da wasu gwamnoni ke ba wa jam'iyyar APC gabanin zaɓen gwamna na ranar 15 ga watan Agusta.
Adeleke ya siffanta kansa a matsayin garnaƙaki kuma sarkin aiki wanda ke da goyon bayan talakawa, inda ya jaddada cewa abokan hamayyarsa ba za su iya murƙushe muradin al'ummar jiharsa ba.
Kasancewar Adeleke a jam'iyyar Accord ya zo ne bayan ficewarsa daga jam'iyyar PDP saboda rikicin cikin gida da ya addabi shugabancin jam'iyyar a matakin kasa. Duk da sauya shekar tasa, rassan jam'iyyar PDP na jihar sun amince su mara masa baya domin ganin ya kai gaci a zaben na ranar Asabar.
A gefe guda, babban kalubale da gwamnatin jihar ke fuskanta shine, bayan da Hukumar EFCC ta kulle asusun banki bisa zargin karkatar da kuÉ—aÉ—e har naira biliyan 11.
Jagoran shirin yaƙin neman zaɓen Adeleke ya zargi hukumar da yunƙurin yin zagon ƙ da kuma shirya bita da ƙullin siyasa domin raunana su gabanin babban zaben.
Haka kuma, an sami taƙaddama ta fuskar tsaro inda rundunar 'yan sanda ta cafke Mayowa Adejoorin, Kwamishinan Muhalli na jihar Osun, sak**akon wani tashin hankali da ya faru a taron yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC.
11/08/2026
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata, lamarin ya auku daga nisan kilomita ɗaya ta ƙasa.
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata, lamarin ya auku daga nisan kilomita ɗaya ta ƙasa.
Yada
An yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja
An ji motsin ƙasa a wasu yankuna na babban birnin tarrayar Nijeriya a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa an yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar a ranar Talata.
Ministan Ma’adinai na ƙasar Dele Alake ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Lara Owoeye-Wise ta fitar ranar Laraba.
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke yankin Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata.
Hukumar ta ce lamarin ya auku ne a yanki mai nisan kilomita ɗaya ta ƙasa kuma ya yi tafiyar kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.
A cewar NGSA, motsin ƙasar ya kai ƙarfin maki 1 zuwa 2 a ma'aunin Mercalli, inda ta bayyana yanayin da mai sauƙi da ba zai iya haifar da lalacewar gine-gine ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.
Sanarwar ministan ta ce tuni aka É—auki matakan gaggawa na gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron lafiya da kadarorin mazauna birnin.
05/08/2026
Hukumar tace Fina-finai ta Jihar Kano ta rufe cibiyar Kausar Unique Empire, wadda aka fi sani da Back to Back, bisa zargin wallafa tallace-tallace marasa É—a'a da amfani da hotuna ko zane-zane na batsa wajen tallata magungunan gargajiya a kafafen sada zumunta.
05/08/2026
Rundunar sojin saman Nijeriya ta kwashe kashi na farko na sojojin Nijeriya da za su shiga rundunar kiyaye zaman lafiya ta ECOWAS a ƙasar Guinea-Bissau.
Rundunar ta tabbatar da wannan ne a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar.