Taskar wasanni tv

Taskar  wasanni tv

Share

Labarin wasanni

30/08/2026

🚨 GA MU ZUWA! AL HILAL TA KAMMALA YARJEJIYAR SAYEN GABRIEL MARTINELLI DAGA ARSENAL 🔵⚪️

An tabbatar da shirin sayen Martinelli da Ollie Watkins, yayin da dan wasan gefen dan Brazil ya samu izinin tafiya Saudiyya.

Kudin da aka cimma ya haura Yuro miliyan 65, kuma Martinelli ya amince da Al Hilal kwanaki da s**a wuce. Za a yi gwajin lafiya domin kammala cinikin.

Ku kimanta wannan sayen daga 1 zuwa 10! ⚡️🇧🇷

Photos from Taskar  wasanni tv's post 30/08/2026

🚨 Xabi Alonso game da Robert Sanchez: "Za mu gani. Shawara ce da muka ga tana da kyau ga ƙungiyar, ga kulub ɗin".

"Wani lokaci dole ne ka yi SHAWARA MAI WUYA domin wannan tana da muhimmanci".

"Yanzu muna bukatar mu kalli gaba" 🔵

29/08/2026

🚨🔵🔴 ATLETICO MADRID BA TA DA IKON HANA SHI — KO FIFA MA! 🤯

Julián Álvarez na iya samun wata hanya ta tilasta komawarsa Barcelona kafin a rufe kasuwar musayar ƴan wasa, duk da cewa Atlético Madrid ta sha nanata cewa ba za ta taɓa tattaunawa da Barça a kansa ba. 😳

A cewar rahoton GiveMeSport, wata tsohuwar dokar Spain mai suna Royal Decree No. 1006 na ba ƙwararren ɗan wasa damar kawo ƙarshen kwantiraginsa da kansa. Idan hakan ta faru, batun diyya zai koma gaban kotu domin a tantance adadin kuɗin da Atlético za ta samu.

Rahoton ya kuma ce FIFA ba za ta iya shiga tsakani ba, saboda wannan lamari ya shafi ƙungiyoyi biyu daga ƙasa ɗaya, kuma batun zai kasance ƙarƙashin tsarin shari'ar Spain.

Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne, rahoton ya ce Barcelona na iya ɗaukar nauyin biyan wannan diyya. Adadin ba lallai ya kai ga €490M na release clause ɗin Julián ba, domin kotunan Spain na iya kallon irin waɗannan manyan release clauses a matsayin masu tsauri.

⏳ Barcelona har yanzu na son cimma yarjejeniya da Atlético kafin 1 ga Satumba, amma idan Atlético ta ci gaba da ƙin tattaunawa, Julián na iya ɗaukar mataki da kansa domin ganin burinsa na komawa Barcelona ya tabbata. 🔵🔴👀

Shin Julián ya kamata ya yi amfani da wannan dokar ya koma Barcelona? 🤯🔵🔴

[GiveMeSport / Mundo Deportivo / GOAL]

29/08/2026

☎️ RASHIN JITUWA TSAKANIN JULIÁN ÁLVAREZ DA ATLÉTICO MADRID!

A cewar rahotanni, tawagar Julián Álvarez ta bai wa Gil Marín wa’adin ƙarshe: ko dai ya taimaka wajen sauƙaƙa ficewar Álvarez daga ƙungiyar, ko kuma su fito fili su bayyana komai a cikin wata hira da manema labarai.

Tawagar ɗan wasan ta yi iƙirarin cewa akwai manyan batutuwa masu muhimmanci da har yanzu ba a bayyana su ga jama’a ba, kuma suna shirye su bayyana dukkan bayanan.

🚨 A halin yanzu, ana gudanar da taron gaggawa tsakanin shugabannin Atlético Madrid, yayin da kulob ɗin ke ƙoƙarin hana lamarin rikidewa zuwa wata babbar badakala a idon jama’a.

28/08/2026

🚨🔵🔴 Yanzu Yanzu: MANCHESTER CITY TA SHIGA TAFIYAR NEMAN JULIÁN ÁLVAREZ! 😳🔥

Manchester City ta shiga gasar neman Julián Álvarez, inda ƙungiyar ke nazarin yiwuwar aro ɗan wasan daga Atlético Madrid domin ƙarfafa harinta bayan tafiyar Marmoush da Savinho. 👀

Rahoton Mundo Deportivo ya ce Arsenal ma na son ɗan wasan, amma Julián yana da shakku game da komawa Ingila bayan yadda ya bar Manchester City shekaru biyu da s**a gabata.

A halin yanzu, Atlético Madrid ba ta shirya tattaunawa kan farashin da bai kai €150M ba. Amma a kwanakin ƙarshe na kasuwar musayar ƴan wasa, komai na iya faruwa. 😳

Abin da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne, duk wannan na faruwa ne yayin da Julián ke son barin Atlético domin komawa Barcelona. 🔵🔴👀

Shin City za ta iya karkatar da Julián daga Barcelona? 🤔

[Mundo Deportivo]

28/08/2026

🚨🔵🔴 Yanzu Yanzu: Magoya bayan Atlético sun fara nuna fushinsu kan rikicin Julián Álvarez! 👀

An sanya wasu sakonni a filin wasa na Metropolitano da ke nuna cewa wasu magoya bayan Atlético sun gaji da halin da ake ciki.

Ga rubutun 👇👇👇

🗣️ “Duk inda zai je, yaje shi, amma dole ya bar ƙungiyar mu YANZU!”

Dayan rubutun ya ƙara da cewar:

🗣️ “Atleti ta fi girman kai naka, Gil Marín!”

🤝 Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Julián da Atlético ke ƙara tsananta, musamman bayan shugabannin kulob ɗin sun dage cewa ba za su bar ɗan wasan ya koma Barcelona ba.

👀 Yanzu har magoya bayan Atlético sun fara matsa wa Gil Marín lamba. Shin wannan saga ɗin na Julián zai ƙare da shi a Barça? 💙❤️

28/08/2026

🚨 Marc Cucurella: "Shin zan yi TATTOO idan muka ci gasar Champions League?" ✒️🏆

"Mu jira mu gani. Dole ne mu CIKA ALKAWARANMU. Mu gani" 😅

Photos from Taskar  wasanni tv's post 28/08/2026

🚨 Walcott game da Tzolis: "Ina son shi sosai, yana tuna min da Alexis Sanchez" ✨

"Akwai wani abu game da yadda yake motsawa da ƙwallon" ⚽💨

"Na yi matukar burge ni, idan ya kara samun lafiyar jiki kuma 'yan wasa s**a kara sanin wasansa, amma ina son abin da na gani ya zuwa yanzu, da gaske ya BURGE NI".

28/08/2026

🚨⚪️ Duk da sabbin rahotanni da labarai a cikin sa'o'i 24 da s**a gabata, matsayin Real Madrid da Endrick bai canja ba: zai ci gaba da zama. ✅

Endrick ba zai tafi ko'ina ba duk da buƙatun da kungiyoyi da yawa s**a yi. 🤍

Shugabannin Real Madrid da Mourinho sun so Endrick ya ci gaba da zama; ba shi da niyyar barin kulob din. ❌

28/08/2026

🚨🔵 Chelsea da AS Monaco sun gudanar da taro ranar Alhamis domin tattauna Lamine Camara a matsayin zaɓi ga tsakiyar filin Chelsea.
AS Monaco har yanzu suna fatan su riƙe Camara, amma suna ci gaba da tattaunawa kan Pape Matar Sarr daga Spurs, kamar yadda aka ruwaito.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Bauchi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Jama'are
Bauchi