04/09/2026
Zaria New Youth Soccer Development Association Hon Shuaibu Abdullahi Mai-Canter Cup Competition 1st Edition 2026.
Opening Match.
GOLDEN CITY F.C 🆚 F.C ZAFAS 🔥
📅 Date: Friday, 4th September 2026
⏰ Time: 4:00 PM
📍 Venue: Nuhu Babajo Stadium, Babban Dodo, Zaria
Come and Watch total football from Grassroot. You are all invited.
31/08/2026
A hukumance: Jerin Yan Wasan Barca 11 Da Zasu Kece Raini da Rayo Vallecano a filin wasa na New Spotify Camp Nou.
Raga 👇
Joan García
Baya 👇
Kounde - Christensen - Cubarsi - Espart
Tsakiya 👇
Bernal - Pedri - Dani Olmo
Gaba 👇
Gordon - Raphinha - Yamal
Shin zaɓin ya yi kyau kuwa?
A ina gyaran yake?
31/08/2026
LOKACI YA YI : Tauraron dan wasan kwallon kafa na duniya Leniol Messi ya yi ritaya daga bugawa kasar ta Argentina wasa.
31/08/2026
RABIU ALI “PELE” YA CI GABA DA RUBUTA TARIHI A KANO PILLARS!
Ɗan wasan Kano Pillars, Rabiu Ali “Pele”, mai shekaru 45, ya sake nuna cewa shekaru ba su isa su hana ƙwararren ɗan wasa ci gaba da taka leda ba.
Pele ya zura ƙwallo a kakar wasa ta 19 wakiltar Kano Pillars, abin da ya sanya shi cikin jerin fitattun ’yan wasan da s**a daɗe suna taka muhimmiyar rawa a ƙungiya ɗaya. 🤯⚽
A lokacin da ’yan wasa da dama s**a yi ritaya, Rabiu Ali har yanzu yana taka leda tare da zura ƙwallaye, yana nuna irin ƙwarewa da ƙaunar da yake yi wa wasan ƙwallon ƙafa.
Rabiu Ali “Pele” — Gwarzon Kano Pillars na gaske. .
31/08/2026
Asuwaju Cup Competition.
A yau an buga wasan karshe na gasar cin kofi mai suna asuwaju cup Competition, wanda aka buga a Filin GSS Yello Gofar Gayan.
Wasan an buga ne Tsakanin Leading Star da Gandujiyya , an tashi wasan 2-1 nasara ga Gandujiyya.
31/08/2026
Dan wasan kwallon kafa na Ranchers Bees Mustafa kido, ya samu rauni a wasan su na jiya da s**a buga da Ikorodu City a jahar lagos.
28/08/2026
SAUYIN SHUGABANCI A ƘWALLON ƘAFAR NAJERIYA!
An samu sabon sauyi a harkokin gudanar da manyan lig-lig na ƙwallon ƙafa a Najeriya, yayin da ake daf da fara kakar NPFL 2026/27.
Rahotanni sun ce an umarci shugabannin NPFL, NNL, NLO da NWFL da su miƙa ragamar gudanar da gasannin ga Chief Operating Officers (COOs) waɗanda ke aiki ƙarƙashin NFF.
Wannan na nufin cewa manyan jami’an da ke kula da waɗannan gasanni za su dakatar da gudanar da ayyukan yau da kullum, yayin da COOs za su karɓi ragamar gudanarwar har sai an bayar da wani sabon umarni.
Haka kuma, idan COO na wata gasa ba ma’aikacin NFF ba ne, za a naɗa wani daga cikin ma’aikatan NFF domin ya riƙe wannan matsayi na wucin gadi.
⚽ Lig-lig ɗin da sauyin ya shafa sun haɗa da:
🔹 NPFL
🔹 NNL
🔹 NLO
🔹 NWFL
Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauye a shugabancin NFF, bayan murabus ɗin wasu daga cikin manyan jami’an hukumar.
Ana kuma danganta sauyin da matakan da ake shirin ɗauka domin sake fasalin tsarin gudanar da ƙwallon ƙafa a Najeriya.
Yanzu babban abin jira shi ne: Ta yaya wannan sabon tsarin zai shafi gudanar da NPFL27, musamman ganin cewa an tsara fara gasar a yau, 28 ga Agusta 2026?
👀 Ku bamu ra’ayinku:
Shin wannan sauyin zai kawo cigaba ne ga ƙwallon ƙafan Najeriya, ko kuwa zai ƙara rikita tsarin gudanar da lig-lig?
28/08/2026
TA TABBATA: Kungiyar kwallon kafa ta Rancher Bees Kaduna ta tabbatar da daukar dan wasa Jamilu Yusuf Onga daga Katsina United.
Jamilu Onga dai ya taka muhimmiyar rawa a kakar da ta gabata inda ya jefa kwallaye masu matukar muhimmanci ga Katsina United yanzu zai jagoranci tawagar Bee a kaka mai zuwa karkashin jagorancin mai horarwa Usman Abdullah.
Wanne fata kuke yiwa Onga a basuwar kaka mai zuwa ?
28/08/2026
The 2026/2027 NPFL starts today
• Champions
🏆
• Top three
1.
2.
3.
• Relegated teams
17.
18.
19.
20.
Let's have your predictions
28/08/2026
SABON LABARI ‼️
Kungiyar Ranchers Bees ta zabi filin wasa na Kaduna Stadium a matsayin filin da za ta rika buga wasanninta na gida.
Kungiyar Ranchers Bees FC, wacce aka daga darajarta zuwa gasar kwanan nan, za ta buga wasanninta na gida a filin wasa na Kaduna Stadium a lokacin kakar wasa ta 2026/27 ta gasar NPFL.