Hausa Update

Hausa Update 🔴 LABARAI DA DUMI-DUMI | WASANNI | DUNIYA | NIGERIA & KETARE

Al'ummar jihar Zamfara sun fito akan tituna suna murna tare da mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu akan nada ...
02/09/2026

Al'ummar jihar Zamfara sun fito akan tituna suna murna tare da mika godiya ga shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu akan nada Sanata Abdul-aziz Yari shugaban yakin neman zabensa.

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu a Neja na tserewa zuwa jamhuriyar Benin saboda matsalar tsaroMazauna ƙaramar hukumar Borgu...
02/09/2026

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu a Neja na tserewa zuwa jamhuriyar Benin saboda matsalar tsaro

Mazauna ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Neja na fara barin gidajensu zuwa Jamhuriyar Benin, sakamakon ci gaba da kai hare-hare da wasu ’yan bindiga ke yi a yankin.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa ɗan takarar jam’iyyar ADC na Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Borgu/Agwara, Murtala Haliru Dantoro, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai.

Dantoro ya ce matsalar tsaro a yankin na ƙara ta’azzara, inda ake halaka mutane, satar mutane, raba jama’a da muhallansu da kuma takaita zirga-zirga da ayyukan noma s**a addabi al’ummomin yankin.

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin “Hire From Nigeria”, da nufin samar da ayyukan yi miliyan ɗaya masu alaƙa da kas...
02/09/2026

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin “Hire From Nigeria”, da nufin samar da ayyukan yi miliyan ɗaya masu alaƙa da kasuwannin ƙasashen waje nan da shekarar 2030.

Shirin zai haɗa ƙwararrun ’yan Najeriya, ma’aikatan fasaha, masu aikin dijital da masu fasaha da kamfanoni da ma’aikata na ƙasashen waje, domin su riƙa samun ayyukan yi daga Najeriya ba tare da sun ƙaura zuwa ƙasashen waje ba.

Gwamnati ta ce za ta mayar da hankali wajen horar da matasa, ba su takardun shaidar ƙwarewa da kuma shirya su domin gogayya a kasuwar aikin duniya.

Daraktan Kuɗi da Harkokin Mulki a Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gwangwaje Babba...
02/09/2026

Daraktan Kuɗi da Harkokin Mulki a Hukumar Raya Kogunan Hadejia-Jama’are, Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso, ya gwangwaje Babban Hadiminsa, Musa Sale Ɗan Zaria, da kyautar sabuwar mota, kuɗi da sabbin kayan sawa.

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Da Kwamitin Zaman Lafiya Sun Fara Sa Ido Kan Zafin Siyasar 2027Farida Abdullahi Zarma Ayau News...
02/09/2026

DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Da Kwamitin Zaman Lafiya Sun Fara Sa Ido Kan Zafin Siyasar 2027

Farida Abdullahi Zarma Ayau News

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da Kwamitin Zaman Lafiya na Ƙasa sun ƙara sa ido kan kalaman siyasa da za su iya haddasa tashin hankali yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

’Yan sanda sun fara bincike kan kalaman kwamishinan Matasa da Wasanni na Borno, Sainna Buba, shugaban Kuje, Samuel Shekwolo, da Sanata Francis Fadahunsi.

Hakan na zuwa bayan Shekwolo ya ce masu adawa da APC su bar Kuje. Daga baya, wasu ’yan daba sun kai hari kan taron Accord Party a Kuje, inda s**a lalata kayayyaki tare da jikkata mutum ɗaya.

ME ZAKU CE?

Wannan dai shi ne saƙon Kashim Shettima ga 'yan Najeriya kan bikin zagayowar ranar haihuwarsaMataimakin shugaban Najeriy...
02/09/2026

Wannan dai shi ne saƙon Kashim Shettima ga 'yan Najeriya kan bikin zagayowar ranar haihuwarsa

Mataimakin shugaban Najeriyar, ya bukaci 'yan ƙasar da ka da su siya masa kyautuka a bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Shettima, wanda ya cika shekaru 60 a ranar Laraba, ya ce masu niyyar yi masa kyauta su yi amfani da kuɗin wajen yin sadaka da kuma kyautata wa mabukata.

Me za ku ce?

Jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta ...
02/09/2026

Jam’iyyun adawa a Najeriya sun fara tsara yadda za su kayar da gwamnatin APC mai mulkin ƙasar ta wajen haɗakar da za ta fitar da ɗan takara ɗaya mai ƙarfi da zai iya gwabzawa da shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

🚨 LAMINE YAMAL YA LASHE KYAUTAR GWANI NA LALIGA A KANON 2025/2026! 🔵🔴✨👕 Wasanni: 154⚽️ Ƙwallaye: 50🎯 Taimakon ƙwallaye: ...
01/09/2026

🚨 LAMINE YAMAL YA LASHE KYAUTAR GWANI NA LALIGA A KANON 2025/2026! 🔵🔴✨

👕 Wasanni: 154
⚽️ Ƙwallaye: 50
🎯 Taimakon ƙwallaye: 45
🏆 Kofuna: 6
🏆 Kopa Trophy: sau 2
🏆 Golden Boy: 1

🔥 Wani babban tarihi kuma ga matashin ɗan wasan Barcelona!

Tattalin arzikin Najeriya na ƙara bunƙasa inda ya nufi dala tiriliyan ɗayaTattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da samun ...
01/09/2026

Tattalin arzikin Najeriya na ƙara bunƙasa inda ya nufi dala tiriliyan ɗaya

Tattalin arzikin Najeriya ya ci gaba da samun bunƙasa a zango na biyu na shekarar 2026, inda GDP ɗin ƙasar ya ƙaru da kashi 4.43 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 4.23 a makamancin wannan lokaci na shekarar 2025 da kuma kashi 3.89 a zangon farko na 2026, a cewar Ma’aikatar Kuɗin Tarayya.

Ma’aikatar ta ce wannan ci gaban ya ɗaga matsakaicin bunƙasar tattalin arzikin ƙasar a farkon rabin shekarar 2026 zuwa kashi 4.16 cikin 100, daga kashi 3.68 da aka samu a makamancin wannan lokacin shekarar 2025. Ta ce kuma ci gaban ya fara yaɗuwa zuwa sassa daban-daban, inda sassa 27 na tattalin arzikin ƙasar s**a samu bunƙasar sama da kashi uku a zangon na biyu, idan aka kwatanta da 23 a bara.

A fannin samar da kayayyaki, masana’antu sun samu bunƙasa da kashi 3.24 cikin 100, daga kashi 1.60 a zangon makamancin wannan na shekarar 2025, yayin da noma ya ƙaru da kashi 4.39 daga kashi 2.82. Haka kuma, ɓangaren ayyuka, wanda shi ne mafi girma wajen tallafa wa tattalin arzikin ƙasar, ya bunƙasa da kashi 4.60 daga kashi 3.94.

Ma’aikatar ta kuma ce ƙarin darajar naira da daidaito a kasuwar canjin kuɗi sun taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin Najeriya idan aka auna shi da dalar Amurka. A cewarta, naira ta samu ƙarin daraja da sama da kashi 12 cikin 100 tsakanin farkon rabin shekarar 2025 da na 2026, lamarin da ya taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin ƙasar da kusan kashi 17 cikin 100 a ma’aunin dalar Amurka.

Ma’aikatar Kuɗin ta ce wannan ci gaba na nuna cewa Najeriya na kan hanyar cimma burin Gwamnatin Tarayya na mayar da tattalin arzikin ƙasar ya kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030. Ta ce Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanya Najeriya cikin ƙasashe 10 da ake sa ran za su fi bayar da gudunmawa ga bunƙasar tattalin arzikin duniya a 2026, yayin da gwamnati ta jaddada buƙatar ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki domin tabbatar da cewa ci gaban ya koma ga talakawa da sauran ‘yan ƙasa.

A gefe guda kuma

Shugaba Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 60

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 a ranar 2 ga Satumba, inda ya bayyana shi a matsayin amintaccen abokin aiki da ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa Borno da Najeriya hidima.

A cikin saƙon taya murnar, Shugaba Tinubu ya taya matar Shettima, Nana, da ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasa murnar wannan gagarumin matsayi. Ya bayyana Shettima a matsayin ɗan kishin ƙasa mai jajircewa, haƙuri da sadaukarwa, tare da yabawa irin rawar da ya taka a harkar banki da kuma lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno.

Tinubu ya ce Shettima ya nuna jajircewa, ƙwazo da tausayi wajen inganta rayuwar al’umma a matsayinsa na Gwamnan Borno, sannan daga bisani a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya. Ya kuma yaba masa bisa biyayyarsa ga jam’iyyar APC da kuma goyon bayan da yake bai wa gwamnatin tarayya wajen aiwatar da ajandar Renewed Hope.

Shugaban ya bayyana cewa a matsayinsa na Shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC), Shettima ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita manufofin tattalin arziki da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi. Ya ce mutunta kundin tsarin mulki, cibiyoyin dimokuraɗiyya, tattaunawa da tuntuba da Shettima ke yi sun taimaka wajen ƙarfafa shugabanci nagari.

Tinubu ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasar bisa amincinsa da goyon bayansa, yana mai cewa zai ci gaba da aiki tare da shi wajen cika alkawuran Renewed Hope ga ’yan Najeriya. Ya kuma yi masa addu’ar Allah Ya ba shi lafiya, hikima da tsawon rai, tare da ci gaba da shiryar da shi da kuma ba shi ikon yi wa Najeriya hidima cikin nasara.

Yadda tawagar Gawuna s**a kaiwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Murtala Sule Garo ziyarar bangirma a shir...
01/09/2026

Yadda tawagar Gawuna s**a kaiwa Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Murtala Sule Garo ziyarar bangirma a shirye shiryen Su na dawowa jam’iyyar APC daga NDC

Hon. Muhammad Badaru Umar
da Hon. Ali Datti Yako, NDC State Deputy Chairman ne s**a jagoranci tawagar a wannan yammaci.

Me za ku ce?

Address

Kano
Kunya

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Update posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share