VOK HAUSA

VOK HAUSA

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from VOK HAUSA, Sport & recreation, Gumel Road, Kano.

Ku kasance tare da Voice of Kano VOK HAUSA Domin Cigaba da samun Ingantattun Labarai Cikin Gaskiya da adalci

Ba San zuciya ba kazafi ko kage
Whatsapp no.090393935610. / 09035683171

26/08/2026

SPONSORED
NI AHMAD SANI AHMAD (Abba Jogana) Dan Takarar Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Gezawa da Gabasawa,
A Jam'iyyar ADC Mai alamar Musabiha.

Ina kira ga Al'umma da suyi watsi tare da karya ta Jita jitar Dake yawo akan cewa Ina Shirin janyewa Wani Dan takara Ko yin hadaka da Wani Dan Takara,

Wannan Kalaman Basu da Tushe Ballanta Mak**a, Kuma Ina Mai sanar da Al'ummar Kananan Hukumomin Gezawa da Gabasawa Cewa NI AHMAD SANI AHMAD Ina Nan Akan bakata, Ta Takarar Majalissar Tarayya Gezawa da Gabasawa.

Kuma Insha Allahu Zamuyi Nasara Domin Ceto Yankin Gezawa da Gabasawa daga Halin da yake ciki.

Nagode Wassalamu Alaikum

15/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Adeleke na kan gaba a Osun Ya bawa jam’iyyar APC Tazara da kuri’u 177,572

Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, na jam’iyyar Accord, ya ci gaba da jagoranci yayin da INEC ke tattara sak**akon zaɓen gwamnan jihar.

Daga cikin wards 303 cikin 332, Adeleke ya samu kuri’u 177,572 (50.5%), yayin da dan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu 158,588 (45.1%).

Dan takarar ADC, Najeem Salaam, na matsayi na uku da 5,917.

Ana ci gaba da tattara sauran sak**ako kafin INEC ta ayyana wanda ya lashe zaɓen.

15/08/2026

YADDA ZABE KE TAFIYA A JIHAR OSUN

07/08/2026

Shugaban tashar Rahma Radio da TV Abuja, Malam Nafiu Yahaya, ya ajiye aikinsa.

Nafiu Yahaya shi ne mutum na farko da ya fara magana a Rahma Radio Kano lokacin da aka buɗe tashar a shekarar 2011, sannan ya kasance cikin waɗanda s**a fara gudanar da Rahma Radio Abuja a shekarar 2021.

A tsawon lokacin da ya yi yana aiki a tashoshin biyu, ya riƙe manyan sassa da muk**ai daban-daban.

Ya kuma gode wa Shugabar Hukumar Zartarwa ta tashoshin, da sauran abokan aikinsa, bisa kyakkyawar zaman tare da s**a yi na tsawon shekaru goma sha biyar.

07/08/2026

Atiku ya koka kan shigar kuɗi cikin asusunsa ba tare da saninsa ba

Tsohon mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan wasu kuɗaɗe da aka tura cikin ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma'a, an ce wani mutum da ba a san ko wanene ba ne ya tura kuɗin tare da rubuta cewa: "Contribution Electioneering Campaign."

Atiku ya ce ba shi ko tawagarsa s**a nemi ko s**a amince da wannan kuɗi ba, yana mai cewa abin ya tayar da tambayoyi kan yadda aka samu bayanan asusun nasa na sirri, wanda ba a bayyana wa jama'a ba.

Ya kuma bayyana cewa idan har bayanan sirrin asusun tsohon mataimakin shugaban ƙasa za su iya shiga hannun wasu ba tare da izini ba, hakan na nuna cewa sirrin kuɗaɗen 'yan Najeriya na cikin haɗari.

Atiku ya yi zargin cewa wataƙila wasu masu damar samun bayanan sirri ne s**a fitar da su, yana mai gargadin cewa hakan na iya jefa masu asusun cikin haɗarin masu garkuwa da mutane, 'yan ta'adda, 'yan bindiga da masu damfara.

Ya ce an sanar da hukumomin tsaro da kuma al'umma game da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke tayar da hankali gabanin zaɓen 2027. Haka kuma ya buƙaci 'yan Najeriya da kada su bari irin waɗannan abubuwa su karkatar da hankalinsu daga manufofinsa na siyasa.

03/08/2026

DA DUMI DUMI: Sanata Rufai Hanga ya fice daga jam'iyyar NDC

Sanatan Kano ta tsakiya kuma mataimakin mai tsawatar da marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Rufai Sani Hanga, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NDC.

A cikin wasiƙar murabus mai ɗauke da kwanan wata 3 ga Agusta, 2026, wadda ya aike wa shugaban jam'iyyar na mazabar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, Hanga ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take.

Sanatan ya bayyana cewa ya ɗauki wannan mataki ne bayan nazari da tunani mai zurfi, yana mai cewa ya bar jam'iyyar ne domin mayar da hankali kan wasu al'amuran rayuwarsa da kuma ci gaban aikinsa.

Hanga ya miƙa godiyarsa ga shugabannin jam'iyyar a matakin mazaɓa, kwamitin gudanarwa da daukacin mambobin NDC bisa irin goyon baya, dama da haɗin kai da s**a ba shi a lokacin da yake cikinta.

Ya kuma buƙaci a cire sunansa daga kundin rajistar mambobin jam'iyyar a matakin mazaɓa, tare da bayyana cewa ya mayar da katin shaidar zama ɗan jam'iyyar NDC.

Sanatan ya yi wa jam'iyyar da mambobinta fatan alheri da nasara a dukkan ayyukansu na gaba.

Sai dai, a cikin wasiƙar murabus ɗin, Hanga bai bayyana ko yana da shirin komawa wata jam'iyyar siyasa ba.

01/08/2026

Rahotanni Sun ce Bayan K**a Matar Da Ake Zargin da Sace Jariri, Sabuwar haihuwa a babban asibitin Gezawa General Hospital.

Gcmx Radio/Tv Taji Ta bakin mai gidan nata Limamin Garin Jama'ar Kwagwar Malam Ibrahim Abdullahi.

Inda ya Tabbatar wa Manema Labarai cewa Yana Kasar Saudiyya domin Gudanar da Ibadar Umrah,
Lokacin da Lamarin Ya Faru. Ya Kuma Tabbatar da cewa Bada Izininsa, Matar ta aikata wannan Abu ba.

Ya Kuma Yi Kira ga Rundunar 'yan Sanda ta Jihar Kano da ta Gudanar da cikakken binkice Tare da Gurfanar da wanda ake Zargi agaban kotu, Domin su fiskanci Hukuncin da ya dace.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an k**a mutane kusan 6 domin gudanar da bincike.

30/07/2026

Masha kata da wannan

30/07/2026

Subahanallah Ikon Allah sai Kallo

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address

Gumel Road
Kano