30/04/2026
⚪️ An ruwaito cewa ‘yan wasan Real Madrid sun fi son Jürgen Klopp sosai fiye da José Mourinho a matsayin kocin su na gaba.
👉 Akwai damuwa a cikin ƙungiyar cewa Mourinho zai iya zama k**ar barazana saboda yiwuwar samun rikice-rikice da ‘yan wasa sak**akon girman kai(ego).
29/04/2026
🚨 LABARI DA DUMI-DUMI: Jürgen Klopp da José Mourinho su ne ‘yan takarar da ake ganin za su zama kocin Real Madrid a kakar wasa mai zuwa.
Real madrid Hausa✍🏾
25/04/2026
Ko Kuna Son Ganin Wannan Haɗin A Kaka Mai Zuwa?
Real Madrid Hausa✍🏾
25/04/2026
Complete Football sun rahoto, a watan Oktoba, Real Madrid ta doke Barcelona kuma ta baiwa ƙungiyar tazarar maki 5 a saman teburin La Liga, amma tun daga wannan ranar komai ya lalace musu.
• Kafin nan, sun rasa wasa ɗaya ne kacal a kowacce gasa da s**a buga, kuma suna gurbi mai kyau a gasar zakarun nahiyar Turai.
• Sai Xabi Alonso ya sauya Vinicius a El Clasico, wanda ya k**a faɗa lokacin da yake barin filin wasa.
• “Tafiya zan yi! Tafiya zan yi! Zai fi kawai idan na bar ƙungiyar nan!”
• Tun daga wannan lokaci, dangantakar sa da Xabi Alonso ta yi tsamari kuma ɗakin sanya tufafin Madrid ya rikice, abun da ya haifar da sallamar kocin wata ɗaya bayan faruwar lamarin.
• Real Madrid ta ɗauko Alvaro Arbeloa, wanda ƙungiyar dake buga gasa mai daraja ta uku ta tsige shi a gasar Copa del Rey a wasan sa na farko, daga nan Bayern Munich ta tsige shi a gasar zakarun nahiyar Turai, kuma zai iya tafiya da tazarar maki 11 tsakanin sa da Barcelona idan s**a samu nasara yau.
• Yanzu Madrid ta ƙara tsintar kanta a gurbi k**ar na bara: Babu kofi, neman sabon mai horas wa, tare da babu wani tabbacin samun ci gaba a kaka mai zuwa.
15/04/2026
🚨 Kylian Mbappé:
“A gare ni, yin wasa a Real Madrid k**ar wata 𝐊𝐘𝐀𝐔𝐓𝐀 ce daga Allah.
Samun damar rayuwa da abin da nake so, yin manyan wasanni, da kasancewa a 𝐌𝐀𝐅𝐈 𝐆𝐈𝐑𝐌𝐀N ƙungiya a duniya.” 🤍
REAL MADRID HAUSA✍🏾
14/04/2026
🚨🚨⚠️ Jude Bellingham ya bayyana a taron manema labarai kafin wasan da Bayern Munich gobe cewa ya sha wahala a Real Madrid saboda iya wasa a wurare daban-daban:
• Matsayinsa ya canza sosai tun daga kakar wasansa ta farko
• Ya fara ne yana wasa gaba a matsayin ɗan tsakiya mai kai hari
• Daga baya aka fi amfani da shi a bangaren hagu yana shiga ciki
• Haka kuma ana sanya shi a matsayi na baya-baya gwargwadon tsarin wasa
• Yana ganin zai iya taka rawar gani sosai a matsayi daban-daban
• Yana ganin wannan sauƙin canzawa yana taimakawa ƙungiya
• Amma hakan yana nufin bai samu damar daidaituwa a matsayi guda ba
• A koyaushe sai ya riƙa daidaita salon wasansa
REAL MADRID HAUSA✍🏾
06/04/2026
An Tabbatar Da Ɗan Wasa Edwardo Camavinga Zai Bar ƙungiyar ƙwallon ƙafa Ta Rea Madrid Kuma Ana Sa Ran Zai Koma Wata Ƙungiya a Gasar Priemier Ingila.
Real Madrid Hausa✍️
21/04/2025
🎖️⚪️ Luka Modrić da Dani Carvajal sun karɓi lambar girmamawa ta Laureus World Team of the Year a madadin Real Madrid.
05/04/2025
An gama. Mun mika gasar a filin wasa na Bernabéu ga Valencia da ke matsayi na 16, wadda kusan kowa ya doke su a kakar nan. Carlo Ancelotti dole ne ya tafi. Watakila shi ne mafi girman koci a tarihin kwallon kafa, amma lokacin sa a kulob din ya kare. Babu abin da zai iya kara bayarwa, kuma ba shi da masaniya akan yadda muke taka leda. Bai san yadda zai hada wannan tawagar da ke cike da taurari ta yi wasa ba. Thank you for everythings Ancelotti.