Rashy.10

Rashy.10

Share

Domin samin labaran Kwallon Kafa
Kasance da rashy.10

20/06/2025

Palmeiras da Inter Miami ne ke a matsayi na 1 da na biyu a rukuni na A a gasar Club World Cup.

Rashy.10

20/06/2025

Leo Messi: "Zamu cigaba da kokarin buga wasan mu. Yau mun nuna ƴar gajiya, amma muna da makaman yaƙi. Mun san cewa wasan mu da Palmeiras ba zai zo da sauƙi ba."

Rashy.10

20/06/2025

Lionel Messi ya ƙara gyara zaman sa a matsayin ɗan wasa na uki mafi yawan cin bugun tazara a tarihin ƙwallon ƙafa.

🥇 1) Juninho Pernambuco [77].
🥈 2) Pelé [70].
🥉 3) Lionel Messi [68].

Guda 9 ya rage. 🔜

Rashy.10

20/06/2025

Manolo Gonzalez (Kocin Espanyol) a cikin wata hira a yan kwanakin da s**a gabata, ya ce: "idan har Joan Garcia ya koma Barcelona to tabbas Zan yanke hannuna guda Daya."

Yanzu dai ya kamata Manolo ya cika alkawari... Mu ganshi tamkar haka. 😂

Rashy.10

20/06/2025

Kocin Manchester United Ruben Amorim yana son maye gurbin Andre Onana da mai tsaron ragar FC Porto Diogo Costa dan kasar Portugal, in ji CaughtOffside.

Rashy.10

20/06/2025

Yanzu Botafago ta karɓi jagorancin rukun na B, bayan ta doke PSG a daren yau.

Rashy.10

20/06/2025

PSG a wasanni uku na baya:🤯

✅ 5-0 vs. Inter.
✅ 4-0 vs. Atlético Madrid.
❌ 0-1 vs. Botafogo.

Abun ban mamaki daga ƙungiyar ƙasar Brazil. 🇧🇷

Rashy.10

20/06/2025

Arsene Wenger: "A cikin duniyar ƙwallon kafa ta zamani inda gudu ke rinjayar fasaha, Messi shine babban ɗan wasan da yake da kamar sihiri da ya rage.

"A yau, Messi ya tabbatar mana da cewa kyawu na gaskiya baya tsufa, kuma baiwar Allah ta gaskiya bata ƙarya!"

Rashy.10

20/06/2025

Ɗan jarida: Ban sani ba ko ka san wannan, amma kana ɗaya daga cikin mafi yawan zura ƙwallaye a duniya, kuma ka zura ƙwallon ka ta 50 a Miami. Kowacce rana, sabon tarihi yana zuwa, yanzu kuma gashi ka dawo kan bugun tazara?

Lionel Messi: "Maganar gaskiya, ban sani ba saboda bata wannan nake ba, ni dai kullum nasarar ƙungiya ta shine farko, amma abu ne mai kyau, ko bahaka ba? Duk da cewa ƙididdiga, ƙididdiga ce kawai, kuma samun waɗannan lambobin a ɓangaren bugun tazara abu na musamman, saboda dabara ce da na taso ina yi tun shekaru da dama da s**a wuce a rayuwa ta ga ƙwallon ƙafa.

"Na kasance ina koyo kuma ina kara ingantuwa kowacce rana, kuma na kasance na zura ƙwallaye da yawa da wannan dabarar. Wani ƙarin kayan aiki ne, kuma abu ne mai kyau ace kana cikin gwaraza mafi kyawu a tarihi."

Rashy.10

20/06/2025

Xabi Alonso: "Raúl Asencio ba zai iya ci gaba da wasan ba, saboda ba yanayi ba ne mai kyau a gare shi, sakamakon yana kan shan magungunan kashe kwayoyin cuta."

Rashy.10

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Jaen Layin Assalam
Kano