23/08/2026
Wike: Ba Na Bukatar Mukami a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe Don Cin Nasarar Tinubu
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa ba ya buƙatar wani mukami a kwamitin yaƙin neman zaɓe na APC domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
23/08/2026
Zaɓen Gwaji A Shafukan Sada Zumunta Tsakanin Ɗan Takarar APC Dana NDC.
Ku bayyana ra'ayoyinku a kasan comment 👇👇👇
23/08/2026
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammadu Sanusi II, PhD, CON, ya karɓi baƙuncin Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a fadarsa da ke Gidan Rumfa, Kano.
Ganawar ta gudana ne a ranar Asabar, 22 ga Agusta, 2026, yayin da shugaban jam’iyyar ya kai wa Mai Martaba Sarkin ziyara.
Shafin Sunusi Dynasty ne ya wallafa hotunan da bayanan ziyarar.
23/08/2026
Da ɗumi-ɗumi: Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce a zahiri an riga an san wanda zai yi nasara a zaɓen 2027, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu na samun ƙarin goyon baya sakamakon sauye-sauyen siyasar ƙasar.
Me za ku ce?
22/08/2026
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika alƙawuran da ta ɗauka, tare da fara ɗora Najeriya kan turbar farfaɗo da tattalin arziƙi. Ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027, inda ya buƙaci mambobin kwamitin su yi aiki domin ganin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen.
Me za ku ce?
22/08/2026
Hull City ta gigita Manchester United da ci 2-0 a wasan farko na kakar wasa
Sabuwar ƙungiyar da ta samu gurbin shiga Premier League, Hull City, ta yi gagarumar nasara bayan ta doke Manchester United da ci 2-0 a wasan buɗe kakar Premier League ta 2026/27.
Semi Ajayi ne ya fara jefa ƙwallo a minti na 17, kafin Nobel Mendy ya ƙara ta biyu a minti na 38, lamarin da ya bai wa Hull City damar samun nasara mai tarihi a kan United.
22/08/2026
Ga jerin sunayen waɗanda za su jagoranci kwamitin yakin neman zaben shugaban ƙasa na shekarar 2027.
22/08/2026
Da ɗumi-ɗumi: Babu sunan Rarara a cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu na 2027!
An fitar da jerin sunayen waɗanda za su jagoranci yaƙin neman zaɓen Tinubu da APC a 2027, amma abin mamaki, ba a ga sunan mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara, a ciki ba.
Rarara dai na daga cikin masu tsananin goyon bayan Tinubu da APC, har ma ya kafa ƙungiyar Tripple R domin tallata ayyukan gwamnati.
Shin kuna ganin ya kamata a saka Rarara a cikin kwamitin?
22/08/2026
Cikin Hotuna: Yadd Sanata Barau I Jibrin ya halarci ta’aziyyar rasuwar dattijon, Marigayi Alhaji Hamza Darma, a gidansa da ke Kwanar Maggi, a yankin Hotoro, cikin birnin Kano.