UM Sport News

UM Sport News

Share

Sport News Channel

Photos from UM Sport News's post 10/08/2026

Kungiyar Kwallon Kafa ta Tawayiya FC dake Mazabar Tudun Murtala a karamar hukumar Nassarawa, wadda ta samu nasarar zama zakara a kakar wasanni ta jahar Kano, ta ziyarci jagoran Jam'iyyar APC na karamar hukumar, Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa, domin nuna masa kofin da su ka dauka ya saka musu albarka.

Wannan ziyarar anyi karkashin jagorancin Auwalu coach Tudun Murtala.

10/08/2026

🚨 𝐁𝐑𝐄𝐀𝐊𝐈𝐍𝐆:
𝐉𝐔𝐋𝐈𝐀𝐍 YADAWO! 🔴⚪️👋🏼

Atlético Madrid ta sanya dan wasan ta na dawo atisaye a safiya yau🕷️👀

Kuna ganin ze zauna ko ze koma Barci!
𝑩𝑨𝑪𝑲 𝑻𝑶 𝑾𝑶𝑹𝑲. 🏋🏼‍♂️

10/08/2026

🏁 FULL TIME
CHANJI FC
0–3
FLAMINGO FC

Photos from UM Sport News's post 10/08/2026

KO KUSAN WANENE ALHAJI MUSTAPHA HALADU MAICITTA (ABU SUHAILA) KUWA?

Daga Wakilinmu

Alh. Mustapha Haladu Maicitta Haifaffen Jahar Kano ne daga Unguwar ɗandago
Shi ba Mukamine dashi a NFF ba kuma ba muqami ne dashi a siyasa ba
Shi kawai shugabane wanda yake da burin ganin son cigaban matasa

A harkar ƙwallon ƙafa, akwai shugabanni da ake gane su da matsayinsu, akwai kuma waɗanda ake gane su da ayyukansu da irin tasirin da suke yi ga rayuwar 'yan wasa. Daga cikin irin waɗannan mutane akwai shugaban Kano Ambassadors FC, Alhaji Mustapha Haladu Maicitta Abu Suhaila.

Alhaji Mustapha Haladu Maicitta ya kasance ɗaya daga cikin masu kishin ƙwallon ƙafa da s**a fahimci cewa, domin a samu makoma mai kyau a wasanni, dole ne a saka jari a cikin matasa da masu tasowa.

Abin da ya fi jan hankali shi ne yadda yake amfani da kuɗinsa da dukiyarsa wajen tallafa wa ƙwallon ƙafa, musamman matasa da 'yan wasa masu tasowa waɗanda suke buƙatar dama, ƙarfafawa da kuma tallafi domin su cimma burinsu.

Ayyukansa ba su tsaya ga magana kawai ba. Ya kafa tarihin Samun kai kungiyarsa samu Matsayin Gasa ta biyu a kasar nan (NNL) Ya taimaka wajen gudanar da gasa da yawwa a fadin jahar Kano, ya tallafa wa 'yan wasa da masu horaswa, bayar da kyaututtuka ga waɗanda s**a yi nasara, tare da ɗaukar wasu nauyin da ke taimakawa wajen bunƙasa ƙwallon ƙafa.

Kwanan nan ma, bayan kammala ABU SUHAILA CUP, ya nuna karamcinsa ta hanyar bayar da kyaututtukan kuɗi da kofuna ga waɗanda s**a zo na farko, na biyu da na uku. Wannan ya ƙara nuna irin yadda yake son ganin 'yan wasa suna samun abin da zai ƙara musu ƙwarin gwiwa.

Haka kuma, ɗaukar nauyin kococi biyu na Kano Ambassadors FC, Ibrahim Hamza (Coach M. Inna) da Aminu Kabiru (Coach M. Aminu), domin zuwa karatun coaching course, wani babban misali ne na irin hangen nesansa. Wannan ba wai tallafi ne na yau kawai ba, illa saka jari ne da zai iya amfani ga ƙungiyar da kuma ƙwallon ƙafa gaba ɗaya na tsawon shekaru.

Ba iya Kano Ambassadors ba Alh. Mustapha Haladu Maicitta Shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta Gwale United wace take kan ganiyarta cikin Samun Nasarori a matakin jahar wanda suke buga gasar Kano State Tofa Premier Wanda izuwa yanzu ba a doke kungiyar ba har yanzu

Shi din ba wani matsayi ne da shi a NFF ba bakuma ɗan siyasa bane dan kasuwa ne mai son harkar kwallon kafa wanda yake da burin son ganin cigaban matasa tare da hanasu shiga munanan ayyuka

A matsayinmu na 'yan jarida da masu bibiyar harkar wasanni, ya dace mu girmama tare da yabawa mutanen da suke amfani da damar da Allah Ya ba su wajen taimaka wa matasa da bunƙasa wasanni.

Alhaji Mustapha Haladu Maicitta Abu Suhaila, muna ganin ƙoƙarinka, muna yaba da gudunmawarka, kuma muna godiya da irin ƙaunar da kake nunawa ga ƙwallon ƙafa da matasanmu.

Ba wai kawai kana gina ƙungiya ba ne; kana taimakawa wajen gina makomar matasa.

Muna maka fatan Allah Ya ƙara maka lafiya, arziki da ikon ci gaba da wannan kyakkyawan aiki.

Alhaji Mustapha Haladu Maicitta Abu Suhaila — shugaba mai aiki, mai kishin matasa, kuma mai zuba jari a makomar ƙwallon ƙafa.

Daga UM Sports Channel.
UM Sport News
Mustapha Haladu

10/08/2026

YAN WASAN 𝐌𝐀𝐃𝐑𝐈𝐃 SUN DAWO 🤍🦸

Atisayen farko ga Diomande da Konaté da Cucurella. Ga kuma Mbappé ya dawo ⚡️

📸 Real Madrid C.F.

10/08/2026

𝐑𝐄𝐏𝐎𝐑𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐅𝐎𝐑 𝐃𝐔𝐓𝐘 😁👍

Hotonsu na farko a wajen daukar atisaye Cucurella da Konaté.

Kun shirya wa wannan haɗin kuwa? 🤍

📸 Real Madrid C.F.

10/08/2026

Kamar Kullum Yau Ma Zamu Fara Posting da Fadin
MUHAMMADU RASULULLAH

09/08/2026

🦅🇳🇬 SAƘON JINJINA GA KOCI ABDUL MAIKABA

Muna Alfahari dakai, kada ka bari rashin nasarar wasan ƙarshe ya karya maka gwiwa. ❤️🦅

Ka yi babban aiki wajen jagorantar Flying Eagles daga matakin rukuni har zuwa ƙarshen gasar WAFU B U20. Wannan ba ƙaramin nasara ba ce, musamman ganin cewa wannan shi ne gasar ka ta farko tun bayan da aka naɗa ka a matsayin Technical Adviser na ƙungiyar.

Wasan ƙwallo ba koyaushe ne sakamakon ƙarshe yake bayyana ingancin aikin koci ba. Ka karɓi ƙungiyar, ka gina musu kwarin gwiwa, ka shirya ’yan wasan, ka jagorance su cikin mawuyacin hali, kuma ka kai su wasan ƙarshe. Wannan abin alfahari ne kuma ya cancanci yabo. 👏🏿🇳🇬

Rashin ɗaukar kofin yau ba zai goge kyakkyawan aikin da ka yi ba. Wannan darasi ne da zai ƙara maka ƙwarewa da ƙarfi wajen fuskantar ƙalubalen da ke gaba.

Ka ci gaba da jajircewa, ka ci gaba da aiki, ka ci gaba da yin imani. Tafiyar ba ta ƙare ba wannan farkon sabon babi ne a gare ka da kuma Flying Eagles.

Mun gode da abin da ka yi wa ƙasar nan. Mun yi alfahari da kai. 🦅💚🇳🇬

Ka ɗaga kai, Koci Maikaba — har yanzu muna tare da kai kuma muna goyon bayanka! ❤️🦅🇳🇬

UM Sport News
NPFL Updates

09/08/2026

😭

09/08/2026

58'
Malawi 1-1 Ghana

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Kano?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Address

Kabuga Janbulo
Kano