25/08/2026
daga Lamasia xuwa duniya
A Wannan Shafin Zamu Dinga Kawo Muku Dukkan Labaran Da S**a Shafi Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.
25/08/2026
daga Lamasia xuwa duniya
25/08/2026
🚨✅️Lamine Yamal ba ya farin ciki da halin da Balde yake ciki, musamman saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakaninsu.
Lamine da Balde abokan juna ne na kud da kud, kuma ana iya ganin irin kusancin da ke tsakaninsu a cikin fili da kuma a wajen fili.
Abbas Abdullahi Wailare
28/11/2025
🚨🎖️ Hansi Flick ya bayyana wa Barcelona cewa manyan guraben da dole ne a siyo a lokacin bazara su ne:
1️⃣ Centre-back mai buga hagu
2️⃣ Winger — ɗan wasan gefe
3️⃣ Striker — gaba mai lamba 9
🔵 Kuma akwai yiwuwar a kawo sabon centre-back tun watan Janairu idan dokar kuɗi ta (fair play) ta bada dama kuma idan s**a samu ɗan wasan da yakeda irin abin da kungiyar ke nema.
25/11/2025
❌🇹🇷 Lewandowski yayi watsi da tayin da Fenerbahçe s**a yi masa.
❌ Lewandowski ba ya son barin Barcelona a watan Janairu.
Yana son ya zauna akalla har zuwa ƙarshen wannan kakar.
✅ Makomar sa a Barça har yanzu a bude take.
Kwantaraginsa zai ƙare ne a ƙarshen kakar nan mai zuwa.
23/11/2025
Gerard Martín: “Kafin wasan, mahaifiyata ta nuna min wasu hotuna tun ina ƙarami ina kallo a nan. Abu ne mai motsa zuciya sosai dawowar mu wannan fili.”
“Cikin waɗannan shekaru biyu ko uku abubuwa sun canza sosai a gare ni. Na dage da aiki, na saka a raina abin da ya kamata in yi, da kwarin gwiwa da aiki, kamar yadda aka saba.”
Yanzu zamu iya cewar Martins ya zamu wuri kenan a Barça duba da namijin ƙoƙarin da yayi jiya a Barça?
23/11/2025
🛑🗣️ Shugaba Joan Laporta a kan dawowar Barça gida:
• “Al’amarin ya zama na gaskiya, mun dawo gida, kuma mun yi hakan tare da abin dandano na ƙwallon kafa mai ban sha’awa. Ina matuƙar farin ciki, kamar dukkan magoya bayan Barça.”
• “Mun yi bikin wannan rana ta musamman, rana da ta nuna farin cikin kasancewa ta ɗan Barça, tare da jin ɗan Barcelona ne ni a jiki. Mun gani a lokacin fara wasan da tsofaffin membobin kulob din nan s**a yi.”
• “Kana tunanin mutanen da ba su tare da mu yanzu, musamman mahaifina wanda ya koya min son Barcelona da al’adun Catalan. Duk lokacin da na kalli wurin da na saba zuwa tare da shi, sai na ji motsin zuciya. Abubuwan da aka shirya sun kasance masu sauƙi, amma masu mutunci sosai. Filin ba a gama ba tukuna; wannan dai kamar zagayen girmamawa ne.”
• “Na ji daɗin ganin memba mai lamba 6 ya fara wasa, tare da memban da ya halarci bikin shekarar 1957.”
• “Saƙon da muke tura shi ne komai yana tafiya daidai. Na tattauna da Magajin Garin Barcelona, ɗaya daga cikin mutanen da s**a ba da gudunmawa wajen dawo da mu.”
• “Muna sa ran kammala North Stand kafin ƙarshen wannan shekarar, kuma cikin 2026 za mu gama mataki na uku gaba ɗaya. Wannan babban abin alfahari ne ga magoya bayan Barcelona, babban aikin da ya fi muhimmanci a tarihinmu.”
• “Ba wai kawai za ka gani bane, amma za ka ji shi. Tsofaffin membobi suna roƙona, su kan ce: ‘Don Allah ku gama shi, muna son mu gani.’”
• “Game da wasa a Montjuic? Za ka ga mutane sun fi kusanci da tawagar. Ba filin tsere ba ne, Montjuic ya yi aiki sosai, amma dawowa gida daban take. Abin motsa rai ne sosai.”
• “Wannan zai dinga inganta matsayinmu a duniya, kuma ina so dukkan magoya bayan Barcelona su more wannan sabon babin.”
23/11/2025
Ernesto Valverde ya ce Lamine Yamal ya fi Messi:
"Lamine Yamal yafi Messi? Ban sani ba... lokaci ne kaɗai zai bayyana. Matsayinsa yana da matuƙar girma."
"Messi shi ne mafi kyau a duniya tsawon shekaru da dama, kuma yana da kwazo mai ban mamaki a kowanne lokaci — a horo, a wasa, a dukkan fannoni."
"Lamine Yamal kuwa har yanzu yana farawa ne. Yana da lokaci, amma wasu lokuta muna mantawa da cewa yaro ne har yanzu."
"A kowane hali, muna magana ne kan ‘yan wasa masu baiwa ta musamman sosai." 💎
22/11/2025
Hansi Flick:
“Tun daaa daɗewa, Lokacin da aka kore ni daga wata ƙungiya a Division 3, A raina nake cewa In Allah ya yarda wata rana zan jagoranci Barcelona a Camp Nou.”
“Shekarun baya da s**a wuce, Na taɓa zuwa Camp Nou nake faɗawa kaina cewa wata rana zan zauna a wannan bencin na Barcelona. Yau gashi wannan buri ya cika a gare ni. Wannan yana nuna cewa jajircewa da aiki tuƙuru na iya kai ka ko ina.”
“Na daɗe ina mafarkin jagorantar wasa a Camp Nou. Lokacin da nake Jamus kullum tunani nake akansa. Masu wannan kulob ɗin suna da kirki sosai. Yanzu gashi na cika burina.”
“Ina da ƙwarin gwiwa sosai game da tawagata saboda na yarda da su — na amince da su — Kuma ina ganin muna da inganci sosai.
22/11/2025
FT: FC Barcelona 4-0 Athletic Club
Lewandowski ⚽
Ferran Torres ⚽⚽
Fermín Lopez ⚽
22/11/2025
ANTAFI HUTUN RABIN LOKACI