👇 Ga Jiga-jigan Labarai 10 Na Barça dake tashe a wannan rana
FC Barcelona Hausa
Sabbin Labarai, Sharhi, da tattaunawa akan FC Barcelona a Hausa ❤️❤️❤️
29/08/2026
🔙🔵🔴 A wannan rana ta 2014, Barcelona ta gabatar da Douglas Pereira a matsayin sabon ɗan wasanta. 👀
Douglas ya koma Barça daga São Paulo a shekarar 2014, kuma ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru 5. Barcelona ta biya €4M, tare da ƙarin €1.5M da zai dogara da wasu sharudda. 💰
Amma akwai wani abin mamaki a bayan wannan cinikin. 👀
Da farko, Barça ta shirya sayen Douglas sannan ta bar shi a São Paulo a matsayin aro. Amma saboda kasuwar musayar ’yan wasa a Brazil ta riga ta rufe, hakan bai yiwu ba, don haka dole ya koma Barcelona kai tsaye.
Haka kuma, Douglas bai kasance zaɓin farko na Barça ba. A lokacin, ƙungiyar ta fi son Juan Guillermo Cuadrado, amma daga baya ta koma kan Douglas.
Sai ga abin da ya fi ban mamaki. 😭👇
Douglas ya buga wasanni 8 kacal na hukuma da Barcelona.
⚽ Kwallaye: 0
🅰️ Assists: 0
🏟️ Wasanni: 8
✅ Nasara: 4
🤝 Canjaras: 4
❌ Rashin nasara: 0
Amma duk da waɗannan wasanni 8 kacal, Douglas ya kasance cikin tawagar Barcelona da ta lashe kofuna 8! 😭🏆
🏆 La Liga ×2
🏆 Copa del Rey ×2
🏆 Champions League ×1
🏆 UEFA Super Cup ×1
🏆 FIFA Club World Cup ×1
🏆 Spanish Super Cup ×1
Wato Douglas ya buga wasanni 8, bai taɓa yin rashin nasara ba, kuma ya tafi da kofuna 8. 😭😂
Ba ya da Champions League saboda ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe ta ba, amma a ƙarshe yana da Champions League medal a cikin tarihin sa na Barcelona. 😂🏆
Daga baya Barça ta rika ba shi aro zuwa ƙungiyoyi daban-daban, kafin daga ƙarshe ya bar ƙungiyar.
🤔 Shin kasan?
Douglas Pereira ya buga wasanni 8 kacal a Barcelona, amma a cikin waɗannan wasannin bai taɓa rashin nasara ba. Kuma ya kasance ɗan wasan Barça a lokacin da ƙungiyar ta lashe manyan kofuna 8. 😭🏆
Ƴan amana, Douglas ya cancanci a kira shi ɗan wasan da ya fi samun kofuna fiye da yadda ya buga wasanni? 😂
[FC Barcelona / Mundo Deportivo / AS]
29/08/2026
🔵🔴 Jesse Bisiwu ya bayyana abin da ya fi burge shi tun zuwansa Barça! 👀🔥
🗣️ Jesse Bisiwu: «Na san cewa koyaushe akwai matsin lamba a ƙungiya k**ar Barça, amma bana ƙoƙarin saka wa kaina wasu tak**aiman manufofi.
Haka kawai halina yake. Wani lokaci mutane suna cewa k**ar ban damu da komai ba, amma ni mutum ne mai natsuwa. Kullum ina ƙoƙarin bayar da iya ƙoƙarina kuma in nuna cewa ina da yakinin abin da zan iya yi.
Wayata ba ta daina ringing ba a cikin waɗannan makonnin. A wasu lokuta ma sai na ajiye ta gefe. Da gaske mutum yana jin girman wannan ƙungiya.» 😳
🗣️ Bisiwu ya kuma ce: «Zan fara koyon darussan Sifaniyanci a cikin ƙungiyar.
Tabbas muna magana da Turanci, amma abubuwa da yawa ana yin su da Sifaniyanci. Ina ganin yana da muhimmanci gare ni in iya sadarwa cikin sauƙi da kowa.»
🎙️ Mai jarida: «Wace ƙasa za ka wakilta: Belgium ko Ghana?»
🗣️ Bisiwu: «A yanzu ina buga wa ƙungiyoyin matasa na Belgium, amma tabbas ina da alaƙa da Ghana ma.
Ina ganin ba shawara ba ce da zan iya yanke wa kaina cikin dare ɗaya. Ina buƙatar yin tunani a kai tare da iyalina da wakilaina.
Marc van Bommel, mai horar da tawagar Belgium, shi ma ya turo min da saƙo. Ya taya ni murnar komawata Barça kuma ya ƙarfafa ni. Ya ce yana bibiyar ci gabana sosai.
Yanzu ya rage gare ni in nuna abin da zan iya.» 🇧🇪🇬🇭
🎙️ Mai jarida: «Wane ɗan wasa ne ya fi burge ka?»
🗣️ Bisiwu: «Raphinha, babu shakka. Ina ganin abin mamaki ne yadda yake bayar da kashi 100 cikin 100 na ƙarfinsa a kowane atisaye.
Lamine kuwa, tabbas ƙwararren ɗan wasa ne. Da irin baiwarsa da salon wasansa, ina matuƙar son samun damar buga wasa tare da shi.» 🔥🔵🔴
Ƴan amana, kuna ganin Bisiwu zai iya zama babban ɗan wasa a Barça? 👀
29/08/2026
🚨🔵🔴 Barça na shirya wa watan Oktoba mai tsananin ƙalubale! 😳🔥
A cikin Barcelona, an riga an tsara cikakken shiri domin tunkarar wahalhalun jiki da ke gabansu, musamman a watan Oktoba.
A wannan watan, Barça za ta fuskanci PSG da Real Madrid a cikin mako guda, tare da wasanni kusan duk bayan kwanaki uku. Kuma ana son a ci gaba da buga su da cikakken ƙarfi ba tare da raguwar kuzari ba. 💪
🏋️ Sabuwar gym ɗin da ake ginawa a ƙasa a Ciutat Esportiva, wanda aka gaggauta kammalawa ta hanyar aikin Benjamin Kugel, ana sa ran zai kasance a shirye zuwa watan Satumba.
📡 Haka kuma, za a sanya na’urorin GPS na musamman ga kowane ɗan wasa, domin a rika auna tazarar da ya yi, yawan gudun da ya yi da ƙarfi, da kuma nauyin da tsokokinsa s**a ɗauka.
Duk waɗannan matakan an ƙara su ne domin Barcelona ta iya yin gogayya a mafi girman mataki. Kuma tuni ana fara ganin bambanci.
A wasan da Barça ta yi da Athletic Bilbao, k**ar yadda rahoton ya bayyana, ya kasance k**ar Barcelona na da ƙarin ɗan wasa a filin wasa, saboda yadda ta fi su ƙarfi ta fuskar jiki. 😳🔥
Wannan na iya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su taimaka wa Barça ta yi nasara a kakar bana.
Wannan shi ne “sa hannun jarin” da ba a cika ganinsa ba, amma zai iya zama mai matuƙar muhimmanci. 👀🔵🔴
🇩🇪 Tsarin Jamusawa ya shiga aiki sosai. Komai ana ƙoƙarin mayar da shi na zamani da na’ura. 👏🔥
Ƴan amana, kuna ganin wannan sabon tsarin kula da lafiyar ’yan wasa zai taimaka wa Barça wajen jure yawan wasanni? 💪🔵🔴
29/08/2026
🚨🔵🔴 Barça ta ɗauki mataki mai tsauri kan Hamza! 😱
🇪🇬 Matashin ɗan wasan Masar, Hamza, an dakatar da shi na ɗan lokaci daga buga wasa, kuma a yanzu ba zai ƙara samun ko da minti ɗaya a filin wasa ba. 👀
👊🔥 Bayan kyakkyawan wasan da ya nuna a lokacin wasannin tunkarar kakar wasa, kulake da dama a Turai sun fara nuna masa sha’awa. Saboda haka, rahoton ya ce Barcelona ta yanke shawarar cewa ba zai sake buga wasa ba har sai ya sabunta kwantiraginsa.
Dalilin? Kuɗin biya ja kaɗau ka nashi yuro miliyan €15M ne kawai! 😳
🇪🇸 Barça na son fara tabbatar da makomar wannan ƙwararren ɗan wasa, domin kare kanta daga yiwuwar rasa shi kan kuɗi kaɗan.
Wannan na daga cikin sabon tsarin gudanarwa na Deco: a kare muradun Barcelona ko ta wace hanya. 🔵🔴
Yanzu wakilan Hamza sun fara aiki domin ganin yadda za a warware batun kwantiragin nasa. 👀🔥
Kuma kafin wasan Barça na gaba ana fatan warware lamarin mai sauki.
Me kuke ganin ya k**ata Hamza ya yi:
Ya sabunta kwantiraginsa ko ya jira wasu tayin daga manyan kulake? 🤔
29/08/2026
👇Kaso 99.99% cikin 100 ba zasu cinka ba; hannun waye wannan?
29/08/2026
🚨🇩🇪 Toni Kroos ya faɗi abin da zai iya ba Madridistas tsoro game da Barça! 😳🔵🔴
🗣️ Toni Kroos: “A yanzu Barcelona ce ƙungiyar da ta fi kowacce zurfin tawaga a Turai, idan aka duba ingancin ’yan wasa da kuma yawan su. Suna da ’yan wasa biyu ko uku da za su iya maye gurbin kusan kowane matsayi, kuma ingancin ya kasance mai girma sosai. 🔵🔴
🗣️ “Matsayi ɗaya da nake ganin suna da ƙaranci shi ne na ɗan wasan gaba, kuma za a warware wannan matsalar da zarar sun sayi Julián Álvarez. Da shi, tawagar za ta zama cikakkiya. 🎯🔥
🗣️ “A matsayina na Madridista, dole in amince cewa ina tsoron wannan Barcelona. Suna da damar lashe Champions League sau uku a jere. A ganina, sun fi ƙungiyar da ta zo ta biyu a duniya, wato PSG, nesa ba kusa ba.” 🏆😳
🔥 Idan har wannan magana ta fito daga tsohon ɗan wasan Real Madrid, to lallai Barça ta fara zama babbar barazana a Turai.
Ƴan amana, kuna ganin Barcelona za ta iya lashe Champions League sau uku a jere? 👀🏆🔵🔴
[Toni Kroos]
29/08/2026
📰🔵🔴 Yadda Guardiola ya sauya Messi zuwa False 9 har ya rikita Real Madrid! 🤯
Lokacin da Pep Guardiola ya fara aikinsa a Barcelona, Samuel Eto’o ne ɗan wasan gaba na asali, yayin da Messi da Henry suke taka leda a gefe, kowannensu a gefen da ya saba. 🔵🔴
Amma a shahararren wasan da Barcelona ta doke Real Madrid 6-2 a Bernabéu, Guardiola ya sauya tsarin. Ya matsar da Eto’o zuwa gefe, sannan ya saka Messi a matsayin False 9.
Sak**akon? 🤯
Guardiola ya tarwatsa tsarin Juande Ramos na Real Madrid ta fuskar dabara, yayin da Messi ke saukowa daga tsakiyar fili yana jawo masu tsaron Madrid, abin da ya buɗe manyan gurare a baya.
A kakarsa ta ƙarshe, Pep ya ƙara zurfafa wannan tunanin. Ya yi amfani da Cesc da Leo a matsayin False 9 guda biyu, sannan ya koma tsarin 3-4-3 wanda ya yi k**a da tsarin Johan Cruyff.
🔥 Daga Eto’o a matsayin ɗan gaba na gargajiya, zuwa Messi a matsayin False 9, sannan zuwa Cesc da Messi tare a gaba.
A cewar Sport, Barcelona ta Guardiola ta buga ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙwallon ƙafa da aka taɓa gani a tarihi, kuma Messi shi ne cikakkiyar fuskar wannan salon da abokan hamayya s**a kasa gano yadda za su dakatar da shi. 🐐🔵🔴
Wane salo ne kuka fi so: Messi a False 9 ko Eto’o a matsayin ɗan gaba na gargajiya? Kuma kuna ganin Flick zai iya kwafar salon nan a bana 👀
[Sport]
29/08/2026
🚨🔵🔴 A HUKUMANCE: AN SAN DUK LOKACIN WASANNIN BARCELONA A CHAMPIONS LEAGUE! 🏆🔥
Barcelona ta samu jadawalin wasanninta guda 8 na matakin League Phase na Champions League, kuma akwai manyan wasanni da za su ɗauki hankali sosai. 👀
Ga cikakken jadawalin:
🏠 MD1: Barça 🆚 Feyenoord | September 9 | 6:45 PM
✈️ MD2: Galatasaray 🆚 Barça | October 13 | 9:00 PM
✈️ MD3: PSG 🆚 Barça | October 20 | 9:00 PM
🏠 MD4: Barça 🆚 Aston Villa | November 3 | 9:00 PM
✈️ MD5: Sabah 🆚 Barça | November 25 | 6:45 PM
🏠 MD6: Barça 🆚 Manchester City | December 8 | 9:00 PM
✈️ MD7: Sporting CP 🆚 Barça | January 20 | 9:00 PM
🏠 MD8: Barça 🆚 Como | January 27 | 9:00 PM
🔥 Daga Feyenoord zuwa Manchester City, sannan PSG da sauran ƙungiyoyi, Barcelona za ta fuskanci gwaji daban-daban kafin a san ko za ta tsallake zuwa matakin knockout.
Wane wasa ne kuka fi jira? 👀🏆🔵🔴
29/08/2026
🚨🔵🔴 MOURINHO: “Mbappe ne ya k**ata a baiwa Ballon D'or ba wanda ya lashe Champions League ko World Cup ba!” 😳🏆
🤣 José Mourinho ya bayyana ra’ayinsa kan wanda ya k**ata ya lashe Ballon d’Or, inda ya ce bai k**ata a bai wa ɗan wasa kyautar kawai saboda ya lashe Champions League ko kuma World Cup ba.
Mourinho ya ce idan ana son bayar da kyautar saboda lashe Champions League, to a ba Luis Enrique Ballon d’Or. Idan kuma saboda World Cup ne, to De la Fuente ma ya cancanci hakan. 😳
Amma a ganinsa, akwai bambanci tsakanin wanda ya lashe manyan gasa da kuma mafi kyawun ɗan wasa a duniya.
“Ba za ka ba da Ballon d’Or saboda ya lashe Champions League ko World Cup ba.”
Ya kuma ce akwai 'yan wasa uku ko huɗu da s**a kai matakin Ballon d’Or, sannan ya ambaci Mbappé a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda s**a yi abin tarihi a wannan bazarar.
Mourinho ya ƙara da cewa Ballon d’Or ya k**ata ya kasance ga irin 'yan wasan da idan sun yi ritaya, duniya za ta ci gaba da kewarsu har abada, k**ar Maradona, Ronaldo Nazário, Messi, Zidane da Matthäus. 👀🔥
Shin kun yarda da Mourinho cewa lashe Champions League ko World Cup kaɗai bai isa mutum ya lashe Ballon d’Or ba? 🤔🏆
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano
700103