Funtua Football Transfer News

Funtua Football Transfer News

Share

Ingantatttun labaran wasannin kwallon kafa na garin Funtua da kewayen ta

03/09/2026

🚨FUNTUA PILLARS TA KARƁI KADA WARRIORS A WASAN SADA ZUMUNTA 🤝🔥

Funtua Pillars FC za ta fuskanci Kada Warriors Kaduna a wani Inter-State Super Friendly da ake sa ran zai tattaro ɗumbin masoya ƙwallon ƙafa a Sama’ila Isa Township Stadium, Funtua.
Wasan zai gudana ne a ranar Jumma’a, 4 ga Satumba 2026, da ƙarfe 4:00 na yamma.

Wannan ba wasa ne da za a kalla matsayin wasan sada zumunta kawai ba. Yayin da wasan zai bawa ƙungiyoyin biyun damar gwada ƙarfinsu da kuma bai wa ‘yan wasa damar nuna abin da suke iya, da alfaharin wakiltar Funtua da Kaduna Wanda shine zai karawa wasan armashi.

Funtua Pillars za ta nemi yin amfani da damar ta wajen nuna ƙarfin ƙungiyar da kuma tabbatar da cewa Sama’ila Isa Township Stadium ba filin da baƙi ke zuwa su yi abin da suke so bane.

Magoya bayan ƙungiyar kuma za su kasance wani muhimmin ɓangare na wannan fafatawa, musamman ganin cewa wasan gida na ba ‘yan wasa ƙarin ƙwarin gwiwa.

Amma a ɗaya gefen kuma, Kada Warriors Kaduna ba zata zo Funtua domin yawon shakatawa ba.
Ƙungiyar zata zo da burin yin abin kirki, domin komawa gida da sakamakon da zai sa a ci gaba da magana a kanta bayan an tashi daga wasan.

FUNTUA PILLARS FC 🆚 KADA WARRIORS KADUNA
📅 4/9/2026
⏰ 4:00PM
🏟️ Sama’ila Isa Township Stadium, Funtua

Mr Sky ✍️

30/08/2026

🚨 KATSINA UNITED: KASHI 80% NA ‘YAN WASAN KUNGIYAR ZA SU ZAMA ‘YAN ASALIN KATSINA CIKIN SHEKARU 3 — CEWAR SHUGAN KUNGIYAR ‼️

Chairman na Katsina United, Alh. SuraJO umar Malumfashi(Sarkin wasan Galadiman katsina), ya bayyana wani babban shiri da kungiyar ke da shi na shekaru uku masu zuwa, inda ya ce burinsu shi ne ganin cewa kashi 70 cikin 100 na ‘yan wasan Katsina United ‘yan asalin Jihar Katsina ne.☺️🔥

A yayin wata hira da wakilin Martaba FM 88.9, Mr Sky, Chairman ya ce kungiyar za ta kara mayar da hankali wajen gano tare da bunkasa matasan da s**a fito daga jihar domin su samu damar taka leda a babbar kungiyar.

Ya ce wannan tsari ba magana ce kawai ba, domin tuni an fara ganin alamunsa a bangaren technical crew, inda ya bayyana cewa kusan kashi 99% na ma’aikatan katsina United‘yan asalin Katsina ne.🔵🟡

Alh. Surao ya kuma bayyana cewa Katsina United ta shiga kakar NPFL 2026/27 da babban buri.

Inda yace
“Target dinmu shi ne lashe Nigeria Premier League ta kakar 2026/2027 Idan ba mu samu damar lashe gasar ba, ba za mu wuce matsayi na biyu ko na uku ba.”

Wannan na nufin Katsina United ba ta shiga kakar bana domin kawai ta tsira daga relegation ba, sai dai domin kalubalantar manyan kungiyoyin NPFL da neman daukar kofin.

Da yake magana kan wasan farko na kakar bana da zakarun NPFL, Rangers International, Chairman ya ce ba sabbin abokin hamayya ba ne a gare su.

Ya bayyana cewa a kakar da ta gabata, Rangers ta sha wahala sosai kafin ta samu damar doke Katsina United a gidanta, yayin da a Katsina kuma kungiyar ta iya rike zakarun gasar.

A cewarsa, fara kakar wasa da zakara wata dama ce ta nuna wa sauran kungiyoyin NPFL cewa:
“Katsina United ta shirya.”

Tare da goyon bayan gwamnatin Jihar Katsina, management na Katsina United na ganin cewa an samu sauyi wajen kula da ‘yan wasa, yanayin aiki da kuma walwalar kungiyar.

Yanzu dai babban buri ya koma kan kofin NPFL, yayin da aka fara kafa tubalin samar da kungiyar da za ta dogara sosai da hazikan ‘yan wasan da s**a fito daga Katsina.

Shekaru uku masu zuwa za su iya zama wani sabon babi a tarihin kwallon kafa na Katsina.

Tambayar ita ce:
Shin Katsina United za ta iya lashe kofin NPFL ⁉️

Mr Sky ✍️

28/08/2026

🚨 FUNTUA, DAURA KO MALUMFASHI: WACE KARAMAR HUKUMA CE GINSHIKIN ƘWALLON ƘAFA A JIHAR KATSINA⁉️

A fagen ƙwallon ƙafa, Funtua, Daura da Malumfashi na daga cikin wuraren da ake ganin suna da muhimmiyar rawa wajen haɓaka ƙwallon ƙafa a Jihar Katsina.

Sai dai tambayar da ke gabanmu ita ce: idan aka ajiye son zuciya da kusanci a gefe guda, wace daga cikin waɗannan ƙananan hukumomi uku ce za a iya cewa ta fi sauran ƙarfi da tasiri a harkar ƙwallon ƙafa Jihar Katsina?.

FUNTUA, DAURA KO MALUMFASHI — wace karamar hukuma ce ta fi sauran samar da ’yan ƙwallo masu yawa a Jihar Katsina?

Wace karamar hukuma ce ta fi samun cigaba a harkar ƙwallon ƙafa a halin yanzu?

Wace daga cikinsu ce ta fi yawan ’yan wasa masu gogewa?

’Yan wasan da s**a taɓa buga gasar manyan kungiyoyi, lig-lig daban-daban ko kuma s**a samu damar taka leda a wajen Jihar Katsina dama duniya ?

Mr Sky ✍️

26/08/2026

🚨LABARI MAI DAƊI: AN SAKI YASIR BATURE BAYAN KWANA 26 A HANNUN MASU GARKUWA😍

Bayan shafe kwanaki 26 cikin fargaba, damuwa da rashin tabbas, a ƙarshe an samu labari mai daɗi game da ɗan wasan ƙwallon ƙafa na UBS FC, Yasir Bature, inda aka tabbatar da cewa an sake shi daga hannun masu garkuwa da mutane.

Yasir ya kasance a hannun masu garkuwa na tsawon kwanaki 26 bayan wasu da ake zargin ’yan bindiga ne s**a tare motar da yake ciki a hanyar Zaria tare da yin awon gaba da shi.

Bayan an samu nasarar biyan kuɗin fansa da masu garkuwar s**a nema, an ce an biya Naira miliyan 5 (₦5,000,000) domin ganin an kuɓutar da Yasir.

Bayan karɓar kuɗin fansar, masu garkuwar sun kai Yasir zuwa garin Zaria sannan s**a sake shi.
A yau, bayan an kai shi Zaria, wasu mutane daga Funtua sun samu damar yin magana da Yasir ta waya, inda aka tabbatar da cewa yana raye kuma ya samu ’yancinsa.

Wannan magana ta kawo babban sauƙi ga iyalansa da kuma dukkan mutanen da s**a shafe kwanaki suna cikin fargaba kan halin da yake ciki.
A halin yanzu, Yasir Bature yana Zaria, inda ake duba lafiyarsa bayan shafe kwanaki 26 cikin mawuyacin hali.

Rahotanni sun nuna cewa a lokacin da yake hannun masu garkuwar, akwai damuwar lafiyarsa, lamarin da ya sa iyalansa da abokansa s**a ƙara shiga fargaba.

Sai dai yanzu abin farin ciki shi ne cewa Yasir ba ya hannun masu garkuwa kuma, ya samu ’yancinsa, kuma yana cikin kulawar mutanen da suke tare da shi a Zaria.

Bayan an kammala duba lafiyarsa, ana sa ran za a dawo da Yasir Bature zuwa Funtua gobe, Alhamis 27 ga Agusta 2026, domin ya sake haduwa da iyalansa bayan kwanaki 26 na wahala da rashin tabbas.

Dawowar Yasir gida zai kasance babban abin farin ciki ga iyalansa, ’yan uwansa, abokan arziki, abokan wasansa da kuma daukacin masoyan ƙwallon ƙafa a Funtua da Katsina.

Allah Ya dawo da Yasir Bature Funtua lafiya kalau. Allah Ya saka wa dukkan waɗanda s**a taimaka wajen kuɓutar da shi da alheri.

MrSky✍️

23/08/2026

🚨 AN FITAR DA JADAWALIN WASANNIN HON TUKUR YUSUF DADDY FOOTBALL COMPETITION 2026

Bayan kammala wasannin Round of 64, an fitar da jadawalin wasannin Round of 32 na gasar Maiden Edition of Hon Tukur Yusuf Daddy Football Competition 2026, wadda ke ci gaba da daukar hankalin masu sha’awar kwallon kafa a Funtua da sauran sassan Jihar Katsina.

A wannan mataki, kungiyoyi 32 da s**a tsallake rijiya da baya a zagayen da ya gabata za su sake fafatawa a fafatawar da ba za ta ba kowace kungiya damar yin kuskure ba, domin samun tikitin shiga Round of 16.
Daga cikin manyan wasannin da aka tsara a wannan zagaye akwai fafatawar Golden Star T/Wada FC da Dortmund BKR FC, U.B.S. FC da Barcelona Maska FC, Real Fijo FC da National Stars FC, da kuma Sevilla FC F/Kwallo da Academy Stars FC.

Haka kuma, idanu za su karkata zuwa fafatawar Leventis FC BKR da Real FC Funtua, yayin da Funtua Stars FC za ta kara da Newcastle Utd FC. A daya bangaren kuma, Young Stars FC za ta kara da FC Planners, yayin da Super Academy FC za ta fuskanci Tiger Boys Academy FC.

Bayan kammala Round of 32, wadanda s**a yi nasara za su samu damar shiga Round of 16, daga nan kuma gasar za ta shiga matakan Quarter Finals, Semi Finals, wasan neman matsayi na uku, kafin a kai ga babban Final.

Wannan yana nufin gasar ta shiga wani mataki mai matukar muhimmanci, inda kowace kungiya ke kallon kowanne wasa a matsayin wata dama ta kara matsowa kusa da kofin.

Wace kungiya kuke ganin za ta kai ga Final, kuma wace za ta daga kofin Maiden Edition na Hon Tukur Yusuf Daddy Football Competition 2026?

Mr Sky ✍️

22/08/2026

🚨 ZA'A GUDANAR DA DRAWS A GASAR HON. TUKUR YUSUF DADDY UNITY CUP 2026 A YAU ASABAR 🔥

Idanuwan masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Funtua da kewaye za su karkata zuwa Funtua Township Stadium a yau Asabar, yayin da ake shirin gudanar da Draws na Round of 32 na gasar Hon. Tukur Yusuf Daddy Unity Cup 2026.

Bayan kammala wasannin zagayen farko da s**a rage yawan ƙungiyoyin daga 64 zuwa 32, yanzu hankalin ya koma kan yadda za a haɗa waɗannan ƙungiyoyi a fafatawar Round of 32.

Babban abin da ke ƙara armashin Draw ɗin shi ne rashin sanin wace ƙungiya za ta haɗu da wata.

Daga cikin ƙungiyoyin da s**a samu gurbin Round of 32 akwai Real Fijo, Super Stars, Super Academy FC, Jabiri United, Academy Stars FC, FC Planners, Dortmund Makera FC, UBS FC, Dutsen Reme Academy FC, New Wikki FC, Real FC, Tudun Wada Strikers FC, Newcastle United FC, Young Stars FC, Funtua Stars FC, National Stars FC da sauran ƙungiyoyi.

Saboda haka, Draw ɗin na yau ba zai kasance wani al’amari na yau da kullum ba; zai iya samar da haɗuwa tsakanin wasu daga cikin ƙungiyoyin da ake ganin suna cikin masu neman kofin, tare da haifar da wasu manyan fafatawa tun kafin a kai matakin Round of 16.

Gasar Hon. Tukur Yusuf Daddy ta riga ta kafa tarihi a Funtua bayan haɗa ƙungiyoyi 64 a bugu ɗaya.

Yanzu, yayin da ƙungiyoyi 32 s**a tsira daga zagayen farko, Draw ɗin Round of 32 zai zama wani muhimmin mataki wajen tsara tafiyar da za ta kai ga matakin ƙarshe na gasar.

Ga ƙungiyoyin da s**a tsallake, yau ce ranar da za su fara sanin irin ƙalubalen da ke gabansu.

Rana: Asabar, 22 ga Agusta, 2026
Wuri: Funtua Township Stadium
Lokaci: 10:00 na safe.

Mr Sky ✍️

21/08/2026

🚨 ACADEMY STARS TA DOKE FUNTUA PILLARS, TA LASHE WAMBAN FASKARI FOOTBALL COMPETITION 2026

Academy Stars ta zama zakarar gasar Wamban Faskari Football Competition 2026, bayan da ta doke Funtua Pillars da ci 1–0 a wasan karshe da aka fafata yau Juma’a, 21 ga watan Agusta 2026, a Samaila Isah Township Stadium, Funtua.

Samaila Customer ne ya zura kwallon da ta bai wa Academy Stars nasarar lashe kofin, inda kungiyar ta kare wasan da nasara sannan ta dauki babban kofi na gasar.

Wasan ya kasance mai matukar daukar hankali, musamman ganin yadda kungiyoyin biyu s**a shiga wasan da tarihi na musamman a wasannin karshe.

Funtua Pillars ta shiga wasan ne da tarihin ba ta taba samun rashin nasara a duk wani final da ta buga ba, amma Academy Stars ta kawo karshen wannan tarihi bayan ta yi nasarar doke ta da ci 1–0.

A bangaren Academy Stars kuwa, wannan nasara ta kara tabbatar da irin karfinta a Samaila Isah Township Stadium, domin kungiyar ba ta taba samun rashin nasara a duk wani wasan karshe da ta buga a wannan filin wasa ba. Daga cikin manyan nasarorin da ta taba samu a filin har da lashe Funtua Premier League.

Da wannan nasara, Academy Stars ta ci gaba da tarihin rashin shan kashi a final a Samaila Isah Township Stadium, yayin da Funtua Pillars ta fuskanci rashin nasara ta farko a wani wasan karshe a tarihinta.

Mr Sky ✍️

21/08/2026

🚨 FUNTUA PILLARS VS ACADEMY STARS A WASAN KARSHE YAU

Funtua Pillars da Academy Stars za su fafata yau juma'a 21 ga watan Augustan 2026 a wasan karshe na Wamban Faskari Football Competition 2026, a wani gagarumin wasa da tarihi da alkaluman kungiyoyin biyu s**a sanya masa armashi na musamman.

Wannan ba kawai fafatawar neman kofi ba ce. Final ne da zai hada kungiyoyi biyu masu wani tarihi mai ban sha'awa a wasannin karshe.

A bangaren Funtua Pillars, kungiyar zata shiga wannan wasan ne da wani abin alfahari: ba ta taba samun rashin nasara a duk wani wasan karshe da ta buga a tarihinta ba. Wannan tarihin ne za ta nemi karewa a yau, yayin da take neman karin kofi a cikin tarihin kungiyar.

Academy Stars kuwa , ita ma tana da nata tarihin na musamman, musamman a Samaila Isah Township Stadium, inda kungiyar ba ta taba yin rashin nasara a duk final din da ta buga a wannan filin wasa ba. Daga cikin manyan nasarorin da aka samu a wannan filin har da lashe gasar Funtua Premier League.

Saboda haka, wasan na yau zai kasance irin fafatawar da kowace kungiya za ta shiga da cikakken kwarin gwiwa, amma kuma da babban buri na kare tarihinta.

Akwai babbar kyauta da ke jiran zakara, inda wanda ya lashe gasar zai tafi gida da ita yayin da kungiyar da ta kare a matsayi na biyu za ta samu tashi kyautar.

Wannan ya kara wa wasan armashi, domin kofin da kuma kudin kyautar suna jiran kungiyar da za ta iya yin abin da ya kamata a cikin mintuna 90.

Funtua Pillars na da tarihin rashin shan kashi a final, yayin da Academy Stars ke da tarihin rashin shan kashi a final a Samaila Isah Township Stadium.

Gasar Wamban Faskari Football Competition 2026 dai tana karkashin daukar nauyin Hon. Hamza Sule Wamban Faskari, dan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar Faskari/Sabuwa/Kankara, wanda ya dauki wannan gasa a matsayin wata hanya ta tallafa wa matasa da bunkasa harkar kwallon kafa.

Mr Sky ✍️

Photos from Funtua Football Transfer News's post 21/08/2026

🚨HARKALLA TA FADA! ADAMU VARDY YA RATTAFA HANNU !! kan cinikin CFA 3,000,000🤝✍🏻

Adamu Vardy Funtua ya zama sabon ɗan wasan Gendarmerie FC ta Niger, bayan ƙungiyar ta cimma yarjejeniya da JST Tahoua kan ɗaukar ɗan wasan na tsawon shekaru biyu. Har zuwa 2028

Gendarmerie FC ta fara da tayin farko, amma JST Tahoua ta yi watsi da shi. An sake gabatar da tayin na biyu, wanda shi ma aka ƙi, kafin daga bisani Gendarmerie FC ta gabatar da tayin na uku, wanda JST Tahoua ta amince da shi.

Bayan cimma yarjejeniyar, Adamu Vardy ya yi gwajin lafiya a Daren jiya 20 Augustar 2026, sannan ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi a yau juma'a🔒

Kuɗin farko na cinikin ya kai CFA miliyan 2.4 ( ₦5.77 million), yayin da akwai ƙarin CFA 600,000 ₦1.44 million )wanda ya sa jimillar kuɗin yarjejeniyar takai CFA 300,000 (₦7.21 million) "Harkalla ta fada 🤝.

A Gendarmerie FC, Adamu Vardy zai riƙa karɓar albashin kimanin CFA 333,000 (₦800,000 thousand)duk wata, tare da kwantiragin shekaru biyu.🔐😍

Wannan ciniki na Adamu Vardy na daga cikin manyan harkallar cinikin ’yan wasa a ƙasar Niger a wannan kakar, sannan kuma yana daga cikin harkallar da s**a fi ɗaukar hankali tsakanin ƙungiyoyi daga Niger da Najeriya.

Gendarmerie FC na daga cikin fitattun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Niger, kuma tana da gogewa a gasannin nahiyar Afirka, inda ta taɓa buga gasannin CAF sau biyar, ciki har da kakar 2024/2025.

Daga JST Tahoua zuwa Gendarmerie FC, Harkalla ta fada 🤝

Mr Sky ✍🏻

20/08/2026

🚨 RIKICIN ALKALAN WASA YA DAWO NLO 2: UNITED YOUTH ACADEMY TA KOKA, KUNGIYOYIN FUNTUA NA NEMAN ADALCI!

“Har yaushe za'a cigaba da kallon Funtua a matsayin baƙuwar gari idan kungiyoyinta s**a buga wasa a Katsina?”

Al’amura na kara ɗaukar sabon salo a gasar NLO 2, yayin da korafe-korafen da s**a shafi yadda ake gudanar da wasannin kungiyoyin Funtua s**a sake kunno kai.

A wani rubutu da United Youth Football Academy Funtua ta wallafa, ƙungiyar ta bayyana matuƙar damuwarta kan abin da ta ce ya faru a wasanninta na baya-bayan nan, inda ta yi zargin cewa an yi mata hukuncin da ba ta gamsu da shi ba, musamman yadda aka bayar da penalty guda uku a lokaci guda a wasan da aka buga jiya.

Wannan korafi dai ba sabon abu ba ne ga masu bibiyar ƙwallon ƙafa a Funtua.

Tun daga gasar NLO 1, kungiyoyin da ke wakiltar Funtua sun sha bayyana damuwa kan yadda suke ganin wasu matakan alkalanci ke nuna musu wariya ko fifita kungiyoyin da ke buga wasa a cikin birnin Katsina.
Yanzu da aka shiga NLO 2, irin wannan korafi ya sake bayyana.

❗ SHIN ME KE FARUWA?
Tambayar da ke kan bakin masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon ƙafa ta Funtua ita ce:

Shin kungiyoyin Funtua za su iya samun cikakken adalci idan aka tura su buga wasa a cikin Katsina?

Ba wai ana cewa dukkan alkalai suna nuna wariya ba ne, amma idan korafe-korafe irin wannan s**a ci gaba da maimaituwa daga kungiyoyi daban-daban, ya kamata hukumomin da ke kula da gasar su tsaya su binciki lamarin domin kawar da duk wata shakka.

Ƙwallon ƙafa ba zata samu ci gaba ba idan ƙungiya ta fara shiga wasa tana tunanin cewa abin da zai faru a filin wasa ya riga ya wuce ikon ƙafarta.

Funtua tana da ƙungiyoyi, matasa da masu hazaka da dama da suke neman dama ne kawai su nuna abin da za su iya.

KIRA GA HUKUMOMIN NLO
A wannan lokaci, abin da ya fi dacewa shi ne hukumar da ke kula da gasar ta NLO ta duba waɗannan korafe-korafe cikin adalci, ta saurari bangarorin da abin ya shafa, sannan ta tabbatar da cewa dukkan kungiyoyi suna samun damar yin takara a ƙarƙashin dokoki iri ɗaya.

Domin idan aka cigaba da samun korafe-korafe ba tare da bincike ko bayani ba, hakan na iya rage amincewar kungiyoyi da magoya baya ga tsarin gasar.

United Youth Football Academy Funtua da sauran kungiyoyin Funtua sun cancanci a saurare su.

Mr Sky ✍️

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Funtua?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Address

Mangwarori Behind NTA Funtua
Funtua