Salisu Muhammad A

Salisu Muhammad A

Share

Idan kunji labarin mutuwa na
Kuyi mun addu'a pls
Forgiveness is better than forgetting

21/08/2026

INNA LIL LAHI WA INNA ILLAIHI RAJU'UN

A madadin ni kaina da iyalaina, Ina mika ta'aziyya ga yan uwa da iyalai, Daraktan Agaji na ƙasa, Shugaban Kungiyar JIBWIS na Jihar Bauchi Sheikh Prof. Zubairu Abubakar Madaki, daraktan agaji na jahar Bauchi da sauran yan agaji a faɗin kasa baki ɗaya bisa rasuwar daya daga cikin manyan yan agaji a matakin ƙasa (National Circular Bierar) Alhaji Ahmad Ibrahim Bauchi.

Wanda tuni aka gabatar masa da janaza a yammacin Alhamis dinnan kamar yadda Shari'a ta tanada.

Allah ya gafarta ma sa, ya haska ka kabarin sa, ya sanya albarka a cikin zuriyarsa, ya kuma sanya Aljanna Firdausi ta zama makoma a gare shi, tare da sauran musulmai muminai da s**a rigaye mu. Amin

20/08/2026

Masuss**atul kazzab yane 🤣

20/08/2026

Maulidi bidi,a ce batada asali a musulumci, asuwaki yafi maulidi 🙌

19/08/2026

Maryam Ibrahim Dan Azumi tazo na 1 a 60 da tafseer a musabukar duniya ta Saudia

18/08/2026

URGENT and Official 🚨🚨
Roberto Carlos recites the Shahada and embraces Islam ❤

Photos from Salisu Muhammad A's post 18/08/2026

URGENT and Official 🚨🚨
Roberto Carlos recites the Shahada and embraces Islam ❤

18/08/2026

Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Brazil da Real Madrid, Roberto Carlos, ya karɓi addinin Musulunci, a cewar rahotannin da s**a fito a ranar Talata.

Rahotonnin sun ce Sheikh Jihad Hammadeh, wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke zaune a São Paulo, Brazil, kuma wanda aka sanya cikin jerin mutane 500 mafi tasiri a duniyar Musulunci, ne ya bayyana hakan.

Sheikh Hammadeh ya ce Roberto Carlos ya daɗe yana hulɗa da shi, kuma kimanin makonni huɗu da s**a gabata ya ziyarce shi tare da furta Shahada, inda ya karɓi Musulunci.

Shin wani fata kuke yiwa Roberto Carlos?

18/08/2026

18/08/2026

KARE KAI UMARNI NE DAGA ALLAH

Na kalli wani bidiyo da ya sani damuwa, wani dan iska ne rike da wata sharbebiyar wuka yana ikrarin sai ya dauki ra¥uwar Sheikh Bello Murtala Asada

Allah Madaukakin Sarki ya umarce mu a cikin Al-Qur'ani Maigirma Suratu Anfal aya ta 60, Allah (T) yace:
وأعدوا لهم ما استطعتم من قوة...
Ma'ana: mu yi tanadin (makamai) kowani iri masu karfi...(don abokan gaba)

Ba daidai ba ne Malamanmu su zauna kamar alalen 'yan iska, ana salwantar da rayukansu masu daraja a banza ba tare da kariya ba, a irin haka muka rasa irinsu Sheikh Ja'afar, Malam Albaniy Zaria, Dan Mashiyya Sokoto (Allah Ya jikansu)

Malami mutum ne mai tsada da daraja a cikin al’umma, yana koyar da addini, tarbiyya da zaman lafiya, tabbatar da tsaron rayukansu abune mai matukar amfani

Ba daidai bane sai Malami ya girma, ya sha wahala da gwagwarmaya ya tara ilimi da zai amfanar da al'umma, sai rana tsaka a turo wasu 'yan iska makiya su salwantar da rayuwarsa, dole a basu kariya, ko kuma a barsu su mallaki abinda zasu kare kansu kamar yadda marigayi Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz yayi

Dokar Nigeria ya bada damar a mallaki bindiga, ba sai Malami ba, duk wanda yake da bukata ya bi tsarin da doka ya tanadar ya mallaki bindigar da zai kare kansa, kar ka yadda wasu 'yan iska su zo su bugeka a banza su gudu

Sheikh Murtala Asada ya burgeni sosai da ya mallaki bindigarsa kuma ya nuna wa duniya, masu tunanin zasu kashe Malam su tsira sun yaudari kansu, duk wanda ya shirya tunkarar Malam da wata cutarwa to ya shirya barin duniya

Muna rokon Allah Ya tsare mana rayuwar Sheikh Asada

17/08/2026

TSORON ALLAH YA FI KOMAI. 🤲🏽

Ya ku Musulmi da Kiristoci, kada ku bari bambancin fahimta ko ra’ayi ya kai ku ga cin mutuncin malamai ko masu wa’azi.

Malam mutum ne, zai iya yin kuskure, amma zagi, ƙiyayya da cin mutunci ba su ne hanyar gyara kuskure ba.

Ku ji tsoron Allah. Ku girmama juna. Idan ba ku yarda da magana ba, ku yi gyara cikin hikima da ladabi.

Allah yana ganin abin da muke faɗa da abin da muke aikatawa. ☝🏽

🤲🏽 Allah Ya shiryar da mu baki ɗaya, Ya sa zaman lafiya da fahimtar juna su dore a tsakaninmu.

Want your business to be the top-listed Gym/sports Facility in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address

Dutsen Alhaji
Abuja